'Yan Ta'adda a Babura 100 Sun Kai Munanan Hare Hare a Jihohi 2 a Arewacin Najeriya

'Yan Ta'adda a Babura 100 Sun Kai Munanan Hare Hare a Jihohi 2 a Arewacin Najeriya

  • Mayakan Boko Haram/ISWAP sun kai hare-hare kan sojoji da jama'a a garuruwa biyar da ke jihohin Borno da Yobe
  • Majiyoyi sun bayyana cewa yan ta'addan sun yi musayar wuta da sojoji a Mafa, sun kuma sace makamai da baburan sintiri
  • Duk da ba a tabbatar da adadin sojojin da aka kashe ba amma wata majiya ta ce jami'an tsaro sun yi nasarar halaka yan ta'adda da dama

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Maiduguri, Borno – ’Yan ta’adda da ake zargin mayakan Boko Haram/ISWAP ne sun kai hare-hare a garuruwa biyar da ke jihohin Borno da Yobe a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan artabu mai zafi, sojoji sun dakile harin Boko Haram da ISWAP a jihohi 2

Maharan sun ƙona motocin kaya, tare da sace makamai bayan sun yi arangama da dakarun sojojin Najeriya.

Jami'an sojojin Najeriya.
Hoton dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @NigeriaArmy
Source: Getty Images

Boko Haram ta kai hare-hare jihohi 2

Rahoton da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa garuruwan da aka kai hare-haren sun haɗa da Mafa, Dikwa, Marte da Ajiri a jihar Borno, sai kuma Katarko da ke jihar Yobe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun fara kai hari ne kan wani shingen dakarun sojoji da ke Mafa, inda suka yi musayar wuta da jami’an tsaro.

Bayan haka, rahotanni sun nuna cewa ’yan ta’addan sun mamaye barikin sojoji da ke garin, inda suka kwashe makamai, harsasai da sababbin babura da aka tanada domin aikin tsaro a daji.

Wani jami’in tsaro ya ce:

“Sun sace makamai, harsasai da sababbin baburan aiki da ake amfani da su wajen sintiri a cikin daji. Adadin yan ta'addan da suka kawo harin ya yi yawa, ya wuce yadda kowa zai iya zato.”

Kara karanta wannan

Dakarun tsaron Najeriya sun harzuka, sun hallaka jagoran 'yan ta'adda a Filato

Sojoji sun hallaka yan ta'adda

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da adadin sojojin da suka mutu a harin ba, amma wata majiyar tsaro ta tabbatar cewa an kashe ’yan ta’adda da dama a fafatawar.

“Sun zo da yawa suna da manyan makamai, amma dakarunmu sun kashe da yawa daga cikinsu,” in ji majiyar.

Wani mazaunin yankin ya ce ba a rasa rayukan farar hula ba, sai dai ’yan ta’addan sun sace kayan abinci da wasu kayayyaki, sannan suka ƙone motocin da ke ɗauke da kaya.

Dakarun sojin Najeriya.
Hoton jami'in rundunar sojin Najeriya. Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

An kashe fararen hula a hare-haren?

“Harin ya faru ne bayan ƙarfe 11 na dare ranar Laraba. Sun bude wuta kan shingen sojoji inda fasinjoji ke jiran bude hanya domin su ci gaba da tafiya.
"Sun sace kayan da za a kai Gambarou da wasu garuruwa, amma har yanzu babu rahoton rasa rai daga fararen hula," in ji shi.

Majiyar ta ƙara da cewa ’yan ta’addan na da matukar yawa, suna dauke da manyan makamai, motocin yaki huɗui tare da babura sama da 100.

Kara karanta wannan

Barazanar ISWAP ta zaburar da jami'an tsaro, sun fara tsefe dazukan jihohi 2

Boko Haram ta kashe sojoji a Borno

A wani labarin, kun ji cewa mayakan Boko Haram sun kai hari tare da kashe kwamandan bataliyar soji ta 202, sojoji biyar da ’yan CJTF uku a jihar Borno.

Lamarin ya faru ne yayin da dakarun sojoji da yan sa'kai suke dawowa daga wani aikin kakkabe sansanonin ‘yan ta’adda da suka gudanar a ranar Juma’a.

Rundunar sojojin ta bayyana cewa dakaru sun yi nasarar kashe da dama daga cikin yan ta'addan, kuma sun bi sawun wadanda suka tsere.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262