Magana Ta Kare, Tinubu Ya Rantsar da Sabon Shugaban Hukumar Zaben Najeriya
- Farfesa Joash Amupitan ya kama aiki a matsayin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta watau INEC
- Hakan dai ya biyo bayan rantsar da shi da Bola Ahmed Tinubu ya yi a Aso Rock da ke Abuja ranar Alhamis
- Shugaban kasa ya bukaci Amupitan ya tafiyar da aikinsa cikin gaskiya da rikon amana, yana mai cewa Najeriya na bukatar zabe mai inganci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya – Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).
An gudanar da bikin rantsuwar ne a yau Alhamis, 23 ga watan Oktoba, 2025 a ɗakin taro na majalisar zartarwa da ke fadar shugaban ƙasa, Abuja.

Source: Twitter
Farfesa Amupitan ya karbi ragamar INEC
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa hakan na zuwa ne mako guda bayan Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Amupitan a matsayin shugaban INEC bayan tantance shi a ranar 16 ga Oktoba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bikin rantsar da Amupitan ya samu halartar wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).
Haka zalika, jagororin majalisar dokokin tarayya karkashin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da kuma manyan jami’an hukumar INEC sun halarci taron.
Shugaba Tinubu ya ja hankalin Amupitan
A yayin rantsarwar, Shugaba Tinubu ya gargadi sabon shugaban INEC da ya yi aiki da gaskiya, rikon amana, da tsoron Allah, yana mai cewa ya zama abin koyi wanda ba za a iya zarginsa da komai ba.
“Nadinka da amincewar da Majalisar Dattawa ta yi da kai sun nuna kwarewarka da yardar da gwamnati, bangaren zartarwa da na majalisa, ta yi da kai.

Kara karanta wannan
Shugaban INEC mai jiran gado ya isa fadar shugaban kasa da ke Abuja, an samu bayanai
"Wannan babban ci gaba ne, kuma ina fatan zaka tunkari wannan aiki mai wahala amma mai albarka da cikakkiyar gaskiya, jajircewa da kishin ƙasa.”
- Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu ya tunatar da cewa Najeriya ta samu ci gaba sosai a tafarkin dimokuraɗiyya tun daga 1999, inda aka ƙarfafa hukumomi da tsarin zaɓe ta hanyar dabaru da gyare-gyare.

Source: Twitter
Shugaban INEC zai karya da zaben Anambra
Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa zaɓen gwamna na ranar 8 ga Nuwamba, 2025 da za a yi a Jihar Anambra zai zama gwajin farko ga sabon shugabancin INEC, in ji Channels tv.
Ya ƙara da cewa:
“Dole ne zaɓenmu ya kasance cikin gaskiya, adalci da amana. Dole mu ci gaba da inganta tsarin zaɓe, mu gyara kura-kuran baya, mu kirkiro sababbin hanyoyi don yau da gobe.
"Don samun amincewar jama’a, dole ne mu kare mutuncin zaɓe. Daga rajista zuwa yakin neman zaɓe, kafafen yada labarai, jefa kuri’a da kirgawa, komai ya zama a fili, cikin lumana, kuma sahihi.”
Akpabio ya ce tsarin zabe ya inganta

Kara karanta wannan
Bola Tinubu zai rantsar da shugaban INEC na kasa, an ji abin da zai fara yi a ofis a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa an samu ci gaba a tsarin gudanar da zaben Najeriya tun bayan kayar da PDP a 2015.
Akpabio ya amince cewa duk da akwai wasu matsaloli da ake fuskanta har yanzu, tsarin zaben kasar nan ya fi yadda yake a baya.
Shugaban Majalisar Dattawan ya fadi haka ne yayin da ake karatu na biyu kan kudirin gyaran dokar zabe ranar Laraba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
