Yadda Najeriya Ta Shigo da Biliyoyin Litar Mai duk da Taimakon Matatar Dangote

Yadda Najeriya Ta Shigo da Biliyoyin Litar Mai duk da Taimakon Matatar Dangote

  • Rahoton hukumar NMDPRA ya nuna Najeriya ta shigo da biliyoyin litar mai na fetur daga watan Agusta 2024 zuwa farkon Oktoba 2025
  • Ta ce mai na cikin gida, musamman na Dangote, ya samar da lita biliyan 6.6 kacal, kashi 31 cikin 100 na jimillar samarwa a cikin watanni 15
  • Hakan ya nuna raguwar shigo da mai da kuma ƙaruwa a samar da shi na cikin gida, alamar cewa Najeriya na zuwa matakin cin gashin kanta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rahoton Hukumar NMDPRA ya bayyana yawan litar mai na fetur da Najeriya ta shigo da shi ya yi yawa a kasar.

Hukumar NMDPRA ta ce kasar shigo da kusan lita biliyan 15 na fetur daga watan Agusta 2024 zuwa farkon Oktoba 2025.

Yawan liar mai da ake shigowa da shi a Najeriya
Shugaban kamfanin Dangote a Najeriya, Aliko Dangote da gidan man NNPCL. Hoto: Dangote Group, NNPC Limited.
Source: Facebook

Kason da Dangote ke dauka na shigo da mai

Kara karanta wannan

Zaben Kamaru: Matasa sun barke da zanga zanga, an yi arangama da 'yan sanda

Rahoton Punch ya ce hakan na zuwa ne duk da karuwar karfin tace mai da kuma samar da man da matatar Dangote ke yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar bayanai, jimillar man da aka samar a cikin wannan lokaci ta kai lita biliyan 21.6, inda kashi 69 cikin 100 daga waje ne, yayin da gidajen tace mai suka samar da sauran.

Rahoton ya nuna cewa kamfanin Dangote na ci gaba da ɗaukar kaso mai yawa a kasuwa, amma har yanzu ’yan kasuwa masu shigo da mai na ƙalubalantar sa da rage farashi.

Hukumar NMDPRA ya fadi yawan litar mai da ake shigo da su Najeriya
Shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed yayin taro a Abuja. Hoto: Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority.
Source: Facebook

Yawan mai da aka shigo da shi Najeriya

Shugaban hukumar NMDPRA , Farouk Ahmed yayin taro a Lagos ya bayyana yawan man da aka shigo da shi Najeriya daga Yuni zuwa 22 ga watan Yulin 2025.

Ya ce:

“A yau, Najeriya ta zama ƙasa mai fitar da kayayyakin mai da aka tace. Tun daga farkon watan Yuni zuwa yau (Yuli 22), mun fitar da kusan tan miliyan ɗaya na fetur a cikin kwanaki 50 da suka gabata.”

Hukumar NMDPRA ta tabbatar da cewa matatar mai ta Dangote tana samar da kimanin lita miliyan 20 na fetur a kowace rana domin kasuwar cikin gida.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun watsa daruruwan shanun sata 200 cikin gonaki, sun bukaci haraji

“Ba tare da wata shakka ba, aikin matatar mai ta Dangote mai ƙarfin ganga 650,000 a rana ya sauya tsarin samar da mai, inda take ba da gudunmawar lita miliyan 20 a kowace rana, kuma tana da damar ƙaruwa a nan gaba.”

- Farouk Ahmed

Haka nan rahoton ya tabbatar da cewa shigo da mai na ƙasa yana raguwa sannu a hankali yayin da samar da shi na cikin gida ke ƙaruwa.

Masana sun ce hakan alama ce da ke nuna cewa Najeriya na kokarin zama mai cin gashin kanta wajen tace mai.

Dangote ya sanya sassan matatarsa a kasuwa

A wani labarin, Alhaji Aliko Dangote ya ce ya shirya sayar da kaso 5 zuwa 10 na hannun jarin matatar shi a kasuwar hannun jari ta Najeriya.

Aliko Dangote ya ce shirin zai bi tsarin kamfanonin simintinsa da sukari, inda ya kara da cewa ba ya son mallakar fiye da kaso 70 na matatar.

Attajirin ya tabbatar da cewa kamfanin na duba yiwuwar samun hadin gwiwa da masu saka jari daga Gabas ta Tsakiya domin fadada matatar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.