Hukumar DSS Ta Yi Babban Kamu a Jihar Kaduna, An Bankado Masu Safarar Makamai

Hukumar DSS Ta Yi Babban Kamu a Jihar Kaduna, An Bankado Masu Safarar Makamai

  • Hukumar DSS ta kama mutane uku da ake zargi da safarar makamai zuwa ga ’yan bindiga a yankuna biyu na jihar Kaduna
  • An gano AK-47 guda biyar, bindigar PKT, gidan harsasai hudu, da alburusai sama da 200 da aka ɓoye cikin buhunan masara
  • Gwamna Uba Sani ya yabawa DSS bisa wannan nasara, yana mai cewa masu laifi ba su da wata mafaka a gwamnatinsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama mutane uku da ake zargi da safarar makamai zuwa ga ’yan bindiga a jihar Kaduna.

Wadanda aka kama sun shiga hannu ne bayan wani samame da hukumar DSS ta gudanar a kananan hukumomin Igabi da Kachia.

Kara karanta wannan

Zaben Kamaru: Matasa sun barke da zanga zanga, an yi arangama da 'yan sanda

DSS ta kama wasu masu safarar makamai a Kaduna
Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) suna bakin aiki. Hoto: @OfficialDSSNG
Source: Facebook

An kama masu safarar makamai a Kaduna

Gidan talabijin na Channels ya rahoto cewa DSS ta kwato bindigogi, harsasai, da wasu kayayyaki masu hatsari daga wadanda ake zargi.

A cewar rahoton, an cafke daya daga cikin wadanda ake zargi, mai shekaru 30, a kan titin Nnamdi Azikiwe Bypass a Igabi, dauke da makamai.

DSS ta ba da rahoto cewa ta kama mutumin da bindigogin AK-47 guda biyu, bindigar PKT daya, alburusai sama da 200, da gidajen harsasai hudu, wadanda aka ɓoye cikin buhunan masara.

Sannan an cafke wasu mutane biyu a Kauyen Doka da ke Kachia, a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, yayin da suke jigilar bindigogin AK-47 guda uku a cikin mota kirar Volkswagen Golf zuwa ga ’yan bindiga.

Kara karanta wannan

DSS ta gano jihohi 2 da 'yan ta'adda ke shirin kai sababbin hare hare

Gwamna Uba Sani ya yaba wa DSS

Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya jinjinawa jami’an DSS bisa wannan nasara, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci aikata laifuffukan da za su kawo rikici a jihar ba.

Ta bakin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Sule Shuaibu (SAN), gwamnan ya godewa shugaban kasa Bola Tinubu da daraktan hukumar DSS, bisa ci gaba da tallafawa tsarin tsaron Kaduna.

“Tsarin samun zaman lafiya ba tare da makami ba da muka assasa yana rage laifuffuka sosai a jihar. Duk wanda ke kokarin tada rikici zai gamu da fushin doka,” in ji gwamnan.

Ya kuma yi gargadi ga masu safarar makamai da su daina, domin gwamnati na bibiyar su a kowane lungu, inji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Matasa sun taso Shugaba Tinubu a gaba, suna so a tsige mamba a hukumar NDDC

Gwamna Uba Sani ya ce babu mafakar 'yan ta'adda a Kaduna
Gwamnan Kaduna, Uba Sani na jawabi a wani taron tsaro da aka gudanar a jihar. Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

DSS na ci gaba da bincike a Kaduna

DSS ta tabbatar cewa bincike yana ci gaba, kuma wadanda ake zargin za su fuskanci cikakken hukunci bayan kammala bincike.

“Ba za mu bari Kaduna ta zama hanyar shiga da fitar makamai ba. Za mu ci gaba da fatattakar su har sai mun kawar da su,” in ji hukumar DSS.

A kwanan baya, dakarun Operation Safe Haven (OPSH) sun kama wani dattijo mai shekaru 62 da ɗansa a Zangon Kataf, dauke da bindigogi 11, gidajen harsasai biyu, da alburusai 60.

Sojoji sun kama makamai a Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dakarun Operation Hadin Kai sun gano tarin harsashi da aka ɓoye a cikin wata mota a hanyar Maiduguri–Kaduna.

Lamarin ya faru ne a wurin binciken sojoji da ke Nafada, hanyar zuwa Gombe, bayan direban motar ya nuna shakku kan wata jakar da aka ba shi ya kai Kaduna.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu, an kama hatsabiban yan bindiga da suka hallaka Sarki Mai Martaba

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa bayan an buɗe jakar, sai aka gano cike take da harsasai masu yawa, abin da ya janyo bincike mai zurfi kan waɗanda ke da hannu a harkar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com