Bayan Artabu Mai Zafi, Sojoji Sun Dakile Harin Boko Haram da ISWAP a Jihohi 2
- Sojojin Najeriya sun dakile hare-haren da ‘yan ta’adda suka yi yunkurin kai wa wasu kananan hukumomin jihohin Borno da Yobe
- Sama da ‘yan ta’adda 50 aka kashe yayin da fiye da 70 suka tsere da raunuka, sannan an samu nasarar kwato makamai da dama
- Rundunar soji ta yaba da jarumtar dakarunta tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da kare iyakokin ƙasar daga kowace barazana
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Dakarun haɗin gwiwa na OPHK sun samu nasarar fatattakar wasu ‘yan ta’adda a yayin da suka kai hari a lokuta daban-daban a yankunan a Borno da Yobe.
Miyagun mutanen dauke da makamai sun kai hari Dikwa, Mafa, Gajibo da Katarko da ke jihohin Borno da Yobe a safiyar Alhamis, 23 ga Oktoba, 2025.

Source: Facebook
Jaridar Zagazola Makama ta wallafa cewa wata majiya daga rundunar soji a Maiduguri ta tabbatar an kai hare-haren tsakanin ƙarfe 12.00 na dare zuwa 4.00 na safe .
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakaru sun kora 'yan ta'adda
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa dakaru sun samu nasarar dakile hare-haren bayan sojoji sun yi artabu mai tsanani da maharan.
Majiyar ta bayyana cewa, sojoji sun kashe ‘yan ta’adda sama da 50 a wuraren da aka kai harin, yayin da aka kwato makamai masu yawa.
Daga cikin makaman da aka kama har da bindigun AK-47 guda 38, bindigogin PKT guda 7, RPG guda 5, da gurneti, tare da harsasai daban-daban masu yawa.
Haka kuma, sama da ‘yan ta’adda 70 da suka jikkata kuma suka tsere yayin da jiragen yakin sojojin sama suka take masu baya.
Rundunar soji ta yabi dakarunta
Dakarun tsaron kasar nan sun yi artabu da yan ta'addan da suka kai farmaki Dikwa da Gajibo, ana tsammanin sun fito daga yankin Kamaru.
Ana kuma ganin miyagun da suka kai hari Katarko sun fito daga yankin Timbuktu Triangle wanda aka dade ana ganinsa a matsayin mafakar ‘yan ta’adda.

Source: Facebook
Dakarun soji sun yi amfani da jiragen yaƙi na rundunar sama da kuma bayanan sirri na wajen kai farmakin da ya kashe maharan da dama.
A yayin artabun, wasu daga cikin sojojin sun jikkata amma suna cikin koshin lafiya, sai dai an samu lalacewar wasu motoci da gine-gine sakamakon a Mafa da Dikwa.
Hukumar sojin Najeriya ta yaba da jarumtar dakarunta, tana mai cewa wannan nasarar ta tabbatar da kudirin rundunar wajen kare yan Najeriya.
Sojoji sun kashe dan ta'adda
A wani labarin, mun wallafa cewa rundunar haɗin gwiwar jami’an tsaron Najeriya ta yi nasarar kashe wani jagoran ‘yan ta’adda da ke Barkin Ladi a jihar Filato bayan wani samame.
Rahotonni sun ce an kama kasurgumin shugaban Yan ta'adda, Idris Idris da ake kira Babawo Badoo, kuma ya fara bayar da hadin kai wajen kokarin kamo sauran abokan aikinsa.
Wata majiya ta bayyana cewa amma ana tsaka da tafiya, sai Badoo ya yi yunkurin kwatar makami daga hannun sojoji, lamarin da ya jawo suka bude masa wuta har ya rasu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


