Dakarun Tsaron Najeriya Sun Harzuka, Sun Hallaka Jagoran 'Yan Ta'adda a Filato

Dakarun Tsaron Najeriya Sun Harzuka, Sun Hallaka Jagoran 'Yan Ta'adda a Filato

  • Sojojin Najeriya sun kashe shugaban ‘yan ta’adda mai suna Idris Idris, wanda aka fi sani da Babawo Badoo
  • Lamarin ya afku ne a lokacin da Badoo ke kokarin kwatar makamai daga hannun sojoji a Jihar Filato
  • An cafke shi tare da makamai a kauyen Lugere, sannan ya amsa laifin jagorantar wasu hare-hare a yankin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Plateau – Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da kashe wani fitaccen shugaban ‘yan ta’adda mai suna Idris Idris, wanda aka fi sani da Babawo Badoo.

Dakarun sun yi nasarar kawo karshen fitinannen dan ta'addan a wani samame da suka gudanar a karamar hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato.

Sojoji sun kashe dan ta'adda
Hoton wasu daga cikin dakarun Najeriya Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Getty Images

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa lamarin ya faru ne bayan cafke wanda ake zargin a wajen kauyen Lugere a ranar 20 ga Oktoba, inda aka samu bindigogi da harsasai a wurinsa.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An gano masu yayata 'labarin kisan kiristoci' a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama dan ta'adda a Filato

Rahoton ya ce binciken farko ya nuna cewa Idris ya taba jagorantar hare-hare da dama a cikin Barkin Ladi da makwabtanta.

Rahoton ya ce ya amsa cewa yana jagorantar wani rukuni na ‘yan ta’adda kuma ya yarda zai nuna wa sojoji maboyarsu da ke Kassa Village, a cikin karamar hukumar Barkin Ladi.

An kashe dan ta'adda a jihar Filato
Hoton taswirar jihar Filato Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sai dai, lokacin da suka isa wajen da 10:20 na dare, wanda ake zargin ya yi ƙoƙarin kwace bindigar soja domin tserewa.

Sojojin da ke tsaron sa sun yi gaggawar dakile yunkurinsa, inda suka harbe shi kuma ya koma ga Mahaliccinsa nan take.

Sojoji na neman 'yan ta'adda

Majiyoyi sun bayyana cewa rundunar ta kaddamar da sabon samame a yankin domin kama sauran abokan harkallar Babawo Badoo.

Haka kuma suna kokarin kwato karin makaman da suke da alaƙa da wannan ƙungiyar, wanda ake amfani da su wajen kai wa jama'a hari.

Kara karanta wannan

'Dan Najeriya ya yi amfani da kayan aikin mace, ya burma kansa a matsala a Ingila

Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa:

“Bayan kashe shi, an ƙara tsaurara bincike a yankin domin tabbatar da cewa babu wata barazana daga sauran ‘yan ta’addan da suka rage.”

Rahoton ya kara da cewa jami’an tsaro suna ƙara yawan sintiri a Barkin Ladi da kewaye domin hana ramuwar gayya da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

Sojoji na sintiri don dakile harin ISWAP

A baya, mun wallafa cewa jami'an tsaro sun fara shiri domin kakkabe duk wani yunkurin 'yan ta'addan ISWAP na kai hari jihojin Ondo da Kogi da aka gano suna shirin yi.

Matakin ya biyo bayan bayanan sirri hukumar DSS ta sami da ke nuna cewa kungiyar ISWAP na shirin kai hare-hare a wasu jihohin Najeriya guda biyu, kuma an gano dabararsu.

Biyo bayan wannan rahoto, hukumomin tsaro sun fara gudanar da ayyukan tsaftace dazuzzuka a cikin jihohin da ake zarginsu, tare da karin sintiri, da neman hadin kan jama'a don dakile harin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng