Barazanar ISWAP Ta Zaburar da Jami'an Tsaro, Sun Fara Tsefe Dazukan Jihohi 2

Barazanar ISWAP Ta Zaburar da Jami'an Tsaro, Sun Fara Tsefe Dazukan Jihohi 2

  • Rundunar soji, ‘yan sanda da DSS sun kaddamar da sintiri a dazuzzuka na Ondo da Kogi don hana harin ta’addanci
  • Wannan ran gadi na zuwa ne bayan da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta ce an samu bayanai a kan harin ISWAP
  • Gwamnatocin Ondo da Kogi sun tabbatar da daukar matakan kariya tare da kwantar da hankalin mazauna jihohin biyu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kogi – Rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka an fara aikin hadin gwiwar jami’an tsaro da su ka hada da sojoji, ‘yan sanda da hukumar DSS da 'yan sinitir.

Jami'an tsaron sun hada kai wajen fara bincike da sintiri a dazuzzuka da dama da ke tsakanin jihohin Ondo da Kogi, domin dakile shirin harin ‘yan ta’addan ISWAP.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An gano masu yayata 'labarin kisan kiristoci' a Najeriya

Sojoji da sauran jami'an tsaro za su tunkari barazanar ISWAP
Wasu daga cikin jami'an sojin Najeriya Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Rahoton da Daily Trust ta samu ya tabbatar da cewa sintirin ya haɗa da jami’an Amotekun, mafarauta da masu tsaron dazuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an tsaro suna sintiri a Kogi da Ondo

Rahotanni sun ce an fara gudanar da aiki na musamman don hana maimaituwar irin harin da aka kai Cocin Katolika ta St. Francis da ke Owo a ranar 5 ga Yuni, 2022.

Wannan mummunan hari, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 40 tare da jefa masu bauta da sauran mazauna jihar a cikin tsananin firgici.

Har da yan sanda a cikin jami'an da ke kokarin dakile harin ISWAP
Hoton Sufeton yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto: Nigerian Police Force
Source: Twitter

Majiyoyi sun tabbatar da cewa wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun riga sun shiga wasu garuruwa a jihohin biyu, suna kafa sansanoni don shirya hare-hare.

An ce jami’an leken asiri sun riga sun gano shirin, kuma sojoji da sauran hukumomin tsaro suna cikin shiri domin dakatar da su.

Wani rahoto daga DSS ta fitar ya nuna cewa an gano yankuna kamar Eriti-Akoko, Oyin-Akoko, da garin Owo a matsayin wuraren da ake shirin kai hari.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe hatsabibin dan bindiga Abu AK da ya shiga gari cin kasuwa

Hukumar ta bukaci karin sa ido da hadin kai daga al’umma wajen dakile barazanar, ta hanyar mika masu bayanan sirri a cikin gaggawa.

Gwamnatocin Ondo da Kogi sun tashi tsaye

Gwamnatin jihar Ondo ta tabbatar da samun wannan rahoto, inda Kwamishinan labarai, Idowu Ajanaku, ya bayyana cewa tuni an dauki matakan tsaro don tabbatar da zaman lafiya.

Ya ce rahoton DSS wani bangare ne na tsarin bayanan sirri da ake musaya a tsakanin hukumomin tsaro domin hana faruwar hare-hare.

Haka nan, gwamnatin Kogi ta bakin Kwamishinan labarai, Kingsley Fanwo, ta tabbatar da cewa ta samu rahoton sirri kuma tuni ta hada kai da DSS, sojoji da ‘yan sanda a kan batun.

Fanwo ya ce:

“Gwamnatin Kogi ba za ta bari ‘yan ta’adda su lalata zaman lafiya da ci gaban da aka samu a jihar ba. Mun karfafa matakan tsaro, musamman a iyakokin jihohin biyu.”

Ya kuma bukaci jama’a da su kwantar da hankali, su kasance masu lura, su kuma kai rahoton duk wani motsi da ake zargi ga jami’an tsaro mafi kusa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wa mota wuta, sun yi awon gaba da ma'aikatan INEC a Kogi

DSS ta gano shirin 'yan ta'adda

A baya, kun ji cewa hukumar DSS ta sanar da cewa ta samu bayanan sirri na tabbatar da cewa kungiyar ISWAP na shirin kai hare-hare a garuruwan jihar Ondo da kuma jihar Kogi.

Takardar sirrin, mai kwanan wata 20 ga Oktoba, 2025, wacce daraktan tsaro na DSS a jihar Ondo, H. I. Kana, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa akwai yankunan da ke cikin hadari.

A cewar takardar, wuraren da ake ganin suna fuskantar haɗari sun haɗa daEriti-Akoko, Oyin-Akoko (Akoko Ta Arewa) da garin Owo a karamar hukumar Owo na jihar Ondo.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng