Fashewar Tankar Mai a Neja: Tinubu Ya Aika Sako ga Iyalan Mutum 30 da Suka Mutu
- Gwamnatin tarayya ta jajanta wa mutanen Neja bisa mummunar gobarar tankar fetur da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 30
- Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya ce lamarin ya sake tunatar da illar rashin bin ka’idojin tsaro yayin da hadurra suka faru
- Gwamnati ta umurci NEMA da NOA su tallafa wa wadanda abin ya shafa da kara wayar da kai don guje wa irin wannan masifa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana alhini da ta’aziyya ga mutanen jihar Neja bisa mummunar gobarar tankar fetur da ta auku a kauyen Essa.
Gobarar, wacce ta afku a kauyen Essa da ke karamar hukumar Katcha, ta yi sanadin mutuwar fiye da mutane 30.

Source: Twitter
Bola Tinubu ya jajanta wa mutanen Neja
Shugaba Bola Tinubu ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka mutu, jihar Neja da Najeriya baki daya a sanarwar da ministan labarai, Mohammed Idris, ya fitar, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sanarwar da aka fitar ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya ce lamarin ya sake jaddada bukatar tsaurara matakan tsaro da bin doka yayin da irin wannan hadari ya faru.
Minista Mohammed Idris ya ce:
“Muna taya gwamnatin jihar Neja da mutanenta alhinin wannan babban rashi. Wannan masifa ta sake nuna mana illar hadarin tankar man fetur da rashin bin ka’idoji a tsakanin al’umma.
Fashewar tankar fetur na girgiza gwamnati
Gwamnatin ta bayyana takaicinta cewa duk da wayar da kan jama’a da gargadi da ake ta yi, har yanzu wasu mutane na rige-rigen dibar fetur daga tankokin mai da suka fadi.
“Rayuwar kowane dan Najeriya na da muhimmanci. Wadannan abubuwa masu ciwo suna tuna mana da bukatar karin kulawa, yin hattara da kiyaye doka a lokacin irin wannan hadari."
- Mohammed Idris.
Gwamnatin Tinubu ta kuma yaba wa gwamnatin Neja, jami’an tsaro da ma’aikatan agajin gaggawa saboda daukin gaggawa da suka kai wajen kashe wutar, ceto wadanda suka ji rauni, da tallafa wa iyalan wadanda suka rasu.

Source: UGC
Tinubu ya ba NEMA da NOA sabon umarni
Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya ba hukumar NEMA umarnin hada kai da gwamnatin jihar Neja wajen ba da tallafin gaggawa da kulawar lafiya ga wadanda abin ya rutsa da su.
Haka kuma, Tinubu ya umurci hukumar NOA da ta kara wayar da kan jama’a musamman a yankunan karkara kan illar dibar man fetur daga tankokin da suka fadi da kuma hanyoyin kare kai.
“Muna addu'a ga wadanda suka mutu, sannan muna ta'aziyya da shiga cikin alhini tare da iyalan wadanda suka mutu a wannan lokaci na bakin ciki.
“Allah ya ji kan wadanda suka rasu, ya kuma ba iyalansu hakurin jure wannan babban rashi.”
- Ministan labarai, Mohammed Idris.
Fashewar tankar fetur a Neja
Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa tankar man fetur ta kife a kan hanyar Bida–Badeggi–Agaie a kauyen Essa na jihar Neja, a ranar Talata, 21 ga Oktoba, 2025.
Mutane da dama da suka taru don dibar fetur daga tankar ne suka mutu bayan wuta ta kama kuma tankar ta fashe, inda wutar ta cinye mutane da kadarorin da ke kusa.
Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadurra ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce har zuwa lokacin fitar da rahotonta, ba a tantance yawan wadanda suka mutu ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


