Davido: Gwamna Ya Dauko Fitaccen Mawaki, Ya ba Shi Babban Mukamin Gwamnati
- Gwamnatin Osun ta nada fitaccen mawakin Najeriya, Davido, a matsayin shugaban asusun tallafawa wasanni na jihar
- Gwamna Ademola Adeleke ya ce wannan nadin zai janyo jari da tallafin masu hannu da shuni don farfado da harkokin wasanni
- Yayin da gwamnati ta cewa za ta gyara filin wasa na Osogbo zuwa matakin Olympic, Davido ya dauki matsaya kan nadin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - Gwamna Ademola Adeleke ya nada fitaccen mawakin Afrobeats, David Adeleke (Davido), a matsayin shugaban asusun tallafawa wasanni na jihar Osun (OSTFund).
Matakin, a cewar gwamnati, zai inganta harkar wasanni ta hanyar janyo masu zuba jari da tallafin masu sha’awar ci gaban wasanni daga cikin gida da waje.

Source: Twitter
An kusa gama ginin filin wasannin Osun
Mataimakin gwamnan jihar, Kola Adewusi, wanda kuma shi ne kwamishinan wasanni, ya tabbatar da wannan nada a yayin wani taron manema labarai a Osogbo, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adewusi ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Adeleke ta dauki alkawarin kammala aikin gyara da sabunta filin wasa na Osogbo zuwa matakin gasar Olympic.
“Aikin gyara da sabunta filin wasa na Osogbo yana ci gaba da tafiya, kuma muna sa ran kammala shi cikin gaggawa domin ya zama filin wasa na zamani.”
- Kola Adewusi.
Ya ce gwamnati ta kusa kammala shirye-shiryen kafa hukumar wasanni ta jihar Osun, wacce za ta kula da gudanar da harkokin wasanni, da ci gaba a fadin jihar.
Davido ya karbi mukamin a gwamnatin Osun
Mataimakin gwamnan ya kara da cewa kafa asusun tallafwa wasanni na Osun zai taimaka wajen janyo goyon bayan masu hannu da shuni da masu sha’awar wasanni a cikin da wajen jihar.
“Davido ya karbi mukamin da farin ciki. Mun yarda cewa rawar da zai taka za ta kawo cigaba da bunkasa harkokin wasanni a Osun,” in ji Adewusi.
Ya kara da cewa wannan tsari zai tabbatar da cewa bangaren wasanni ya samu kudin gudanarwa dogon lokaci, ba tare da dogaro da gwamnati kadai ba.

Source: Instagram
Osun za ta zama cibiyar wasanni ta kasa
Jaridar Punch ta rahoto gwamnatin Osun ta kuma tabbatar da cewa da zarar an kammala gyaran filin wasa na Osogbo, zai zama cibiyar karbar gasar kasa da kasa.
“Manufar Gwamna Adeleke ita ce mayar da Osun cibiyar wasanni ta Afirka, domin mu karbi gasa daga kowace kasa,” in ji Adewusi.
Davido, wanda asalin dan jihar Osun ne, zai jagoranci kwamitin da ke da alhakin janyo jari, tallafi, da gudanar da asusun wasanni don ganin jihar ta kai matakin duniya.
Martanin Gwamna Adeleke kan shiga ADC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi magana kan batun sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar ADC.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Gwamna Adeleke ya bayyana cewa akwai mutanen da ke tsoron karbuwar da ya samu a wurin jama'a.
Gwamnan jihar na Osun ya kuma tabbatar da cewa zai tsaya takara a zaben gwamna na shekarar 2026 a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

