Gwamnoni 19 Sun Hada Baki Sun Yi Magana kan Mutuwar Sama da Mutane 40 a Jihar Neja
- Gwamnonin Arewa sun yi alhinin rayukan da aka rasa a mummunan hatsarin tankar mai da ya faru a jihar Neja
- Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ya mika sakon ta'aziyya ga iyalai da gwamnatin Neja
- Ya bukaci jama'a su hada kai da gwamnati da hukumomin tsaro domin daukar matakan hana sake faruwar irin wannan bala'i a gaba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Minna, Jihar Neja – Gwamnonin Arewa 19 karkashin kungiyarsu ta Northern States Governors’ Forum (NSGF) sun nuna damuwa kan fashewar tanka a jihar Neja.
Gwamnonin sun bayyana babban alhini da bacin rai bisa ibtila'in fashewar tankar man fetur da ya faru a kauyen Essa da ke cikin karamar hukumar Katcha ta jihar Neja.

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta tattaro cewa adadin mutanen da suka mutu a fashewar tanka a jihar Neja sun kai 42, wasu sama da 60 sun jikkata.

Kara karanta wannan
'Dan Najeriya ya yi amfani da kayan aikin mace, ya burma kansa a matsala a Ingila
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin Arewa aika sako ga Bago
Gwamnonin jihohi 19 da ke Arewacin Najeriya sun yi jimami da ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu a wannan mummunan lamari da ya faru jiya Talata.
Shugaban kungiyar kuma Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana bakin ciki matuƙa kan wannan bala’i da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da raunata wasu.
A madadin gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya ya mika ta’aziyya ga Gwamnan Neja, Mohammed Umar Bago, da mutanen jihar baki ɗaya, musamman iyalan da suka rasa ’yan uwansu a wannan mummunan lamari.
Daily Trust ta rahoto Gwamna Inuwa na cewa:
“Wannan lamari abin takaici ne kuma mai zafi ƙwarai. Zuciyarmu tana tare da iyalan da suka rasa ’yan uwansu da dukkan jama’ar jihar Neja a wannan lokaci na jimami.”
An gargaji mutane kan dibar mai daga tanka
Gwamna Inuwa ya gargaɗi jama’a da su guji taruwa ko diban mai lokacin da irin waɗannan hatsarori suka faru, yana mai cewa hakan na iya jawo ƙarin asarar rayuka.
"Wannan abu ya sake tunatar da mu muhimmancin ɗaukar matakan tsaro da wayar da kai game da haɗarin sufuri da jigilar kayan fashewa.
"Ya zama wajibi gwamnati, hukumomin da ke kula da harkar tsaro da kuma jama’a su haɗa kai domin hana irin waɗannan abubuwan faruwa nan gaba.”

Source: Facebook
Gwamnan ya kuma yaba da ƙoƙarin jami’an ceto, ’yan sanda da ma fararen hula da suka shiga aikin ceto wadanda suka tsira da bayar da taimako cikin gaggawa.
A ƙarshe, Inuwa Yahaya ya yi addu’a ga Allah ya jikan waɗanda suka rasu tare da neman waraka ga waɗanda suka jikkata.
Yadda tanka ta fashe a jihar Neja
A wani labarin, kun ji cewa wata tanka makare da mai ta fashe a kan titin Agaie zuwa Bida a jihar Neja da yammacin Talata, 21 ga watan Oktoba, 2025.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya haddasa cunkoson ababen hawa mai tsanani a babbar hanyar, inda motoci suka makale na sa’o’i da dama.

Kara karanta wannan
Gwamna ya bi sahun Peter Mbah ya koma jam'iyyar APC mai mulki? Gaskiya ta bayyana
Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Neja ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce mutane da dama sun rasa rayukansu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
