Shehu Sani Ya Hango Matsalar da Za a Fuskanta idan Tinubu Ya Gaza a Mulkin Najeriya
- Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya a majalisa, Shehu Sani ya yi tsokaci kan irin siyasar da ake gudanarwa a Najeriya
- Sanata Shehu Sani ya nuna takaicinsa kan yadda ake zafafawa wajen siyasa wanda hakan ya sa 'yan siyasa ke yi wa juna kallon abokan gaba
- Hakazalika tsohon sanatan ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na da damar sake fasalin kasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi magana kan mulkin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Shehu Sani ya bayyana cewa idan Shugaba Tinubu ya gaza cimma nasara a mulkinsa, zai yi wuya ga duk wani shugaban da zai zo bayansa ya iya tafiyar da Najeriya yadda ya kamata.

Source: Facebook
Shehu Sani ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a tashar TVC a ranar Talata, 22 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Shehu Sani ya ce kan Tinubu?
Tsohon sanatan ya ce Tinubu na da damar zai iya amfani da ita wajen sake fasalin makomar Najeriya, musamman a wannan lokaci da kasar ke kan hanya mai cike da kalubale da bukatar jagoranci mai karfi da hangen nesa.
“Najeriya tana kan wani mataki mai muhimmanci na tarihi, kuma Shugaba Tinubu yana da damar da zai iya amfani da ita wajen sake fasalin kasar. Idan ya gaza, zai zama da wuya a samu wanda zai iya gyarawa daga baya."
- Shehu Sani
Shehu Sani ya koka kan siyasar Najeriya
Tsohon sanatan ya koka da yadda siyasar Najeriya ta munana, sakamakon yadda ’yan siyasa ke daukar juna a matsayin abokan gaba maimakon abokan gina kasa.
“A Najeriya, masu mulki suna kallon ’yan adawa a matsayin makiya, sannan masu adawa ma suna kallon gwamnati a matsayin makiya. Idan siyasa ta zama haka, kasa ba za ta ci gaba ba."
- Shehu Sani
Ya ce wannan halin yana haifar da siyasar yaki da adawa maimakon gudanar da mulki.
“A Najeriya, muna daina magana kan zabe ne kawai bayan shekara daya da kammala kada kuri'a. Daga shekara ta biyu, ana fara kamfen na gaba. Wannan ne yasa kusan kashi 80 cikin 100 na mulkin kowace gwamnati ake cinyewa wajen shirin zabe, ba mulki ba.”
- Shehu Sani

Source: Twitter
Hakazalika ya kuma shawarci Shugaba Tinubu da ya daina kallo ta fuskar siyasa wajen nada mukamai, ya dauki kwararru daga kowane bangare na kasar don gina gwamnati mai nagarta.
Shehu Sani ya ba Jonathan shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya ba tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, shawara kan zaben shekarar 2027.
Shehu Sani ya bukaci Goodluck Jonathan ka da ya ce zai sake jaraba sa'arsa wajen tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben da ake tunkara.
Tsohon sanatan ya bayyana cewa jam’iyyar PDP, wadda Jonathan ya yi amfani da ita wajen lashe zaɓen 2011, yanzu ba ta da haɗin kai kamar yadda take da shi a baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


