‘Kun Yi Kadan’: Sanusi II Ya Kuma Gargadin Masu Neman ‘Rusa’ Kano da Tarihinta

‘Kun Yi Kadan’: Sanusi II Ya Kuma Gargadin Masu Neman ‘Rusa’ Kano da Tarihinta

  • Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana muhimmancin tarihi a Kano da ma Arewacin Najeriya baki daya domin adana al'adu
  • Sanusi II ya ce ba mai iya rusa tarihin Kano, wanda aka gina bisa ilimi, kasuwanci da ƙwarewa ta musamman
  • Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su riƙa rubuta tarihinsu da kansu, yana mai cewa idan ba su yi ba, wasu za su ɓata ma’anarsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi magana kan muhimmancin tarihi da rubuta shi musamman a Arewacin Najeriya.

Sarki Sanusi II ya bayyana cewa babu wanda zai iya lalata tarihin Kano wanda aka gina bisa jajircewa da gaskiya tare da ba al'umma shawara game da tarihinsu.

Sanusi II ya bayyana muhimmancin rubuta tarihi
Sarki Sanusi II yayin ran gadi a Kano. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Source: Twitter

Sanusi II ya halarci taron kaddamar da littafi

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya hango matsalar da za a fuskanta idan Tinubu ya gaza a mulkin Najeriya

Ya bayyana hakan ne yayin gabatar da littattafan Dr. Munzali Dantata a Abuja, wanda suka nuna tarihin rayuwar attajirai na Kano, cewar rahoton Aminiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin ya ce idan ana maganar tarihin Kano, to ya samo asali ne daga ginshiƙan ilimi, addini, da kasuwanci da suka kafa tushe mai ƙarfi ga Arewa.

Sanusi II ya ce:

“Mun zo nan don murna, kuma muna taya kanmu farin ciki, Kano ta ginu ne bisa ƙwarewa da sadaukarwa.
“Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne muna taya jihar murna, birnin wanda ya samar da iyalan Dantata da wasu daga cikin attajiran Nahiyar Afirka.
“Kano ta ginu ne a kan ginshiƙai na ƙwarewa, a addini, ilimi, kasuwanci, kamar yadda na taɓa faɗa a baya, duk wanda ke tunanin zai iya rusa Kano ɓata lokacinsa yake yi, ba zai taba yin nasara ba.”
Sanusi II ya ce babu wanda zai iya rusa Kano
Sarki Sanusi II yayin bikin kammala digirin digirgir a London. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Twitter

Sarki Sanusi II ya ba al'umma shawara

Sarkin ya yi kira na musamman ga mazauna Arewa, da su yi kokarin rubuta tarihinsu domin kare martabarsu a duniya, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: ACF da Afenifere sun aika sako ga sojojin Najeriya

Ya yabawa gudunmawar da iyalan Dantata suka bayar a fannin tattalin arzikin jihar da bangaren girmamawa da aiki tukuru.

Ya kara da cewa:

“Kiran da nake yi shi ne, mu riƙa faɗin labarinmu da kanmu, ba za a iya magana kan tarihin Kano ba, ba tare da dangin Dantata da sauran ’yan kasuwanta ba.”

Mawallafin littafin, Dr. Munzali Dantata ya ce littattafan sun bayyana ƙoƙarin ci gaban Kano da kuma yadda aka samu haɗin kai wajen gina kasuwanci.

Ya ce:

“Waɗannan littattafai nawa labarai ne guda biyu; akwai na mutum ɗaya da ɗaya kuma na al’umma, amma duk suna ɗauke da ƙoƙarin ci gaban kasuwanci."

Sanusi II ya yaba salon mulkin Tinubu

Mun ba ku labarin cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi ruwan yabo ga gwamnatin Bola Tinubu ke ɗauka don farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.

Khalifa Sanusi II, wanda tsohon Gwamnan CBN ne ya ce cire tallafin mai da daidaita farashin Dala da Naira sun taimaka wa Najeriya.

Mai Martaban ya bayyana cewa tattalin arziki na nuna alamun farfaɗowa, duk da buƙatar ƙarin gyare-gyare da ba za a rasa ba a yanzu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.