An Rasa Rayuka bayan Sojoji Sun Fafata da 'Yan Bindigan da Suka Zo Daukar Fansa a Zamfara
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki kan dakarun sojojin da ke aikin samar da zaman lafiya a jihar Zamfara
- Miyagun 'yan bindigan sun kai harin ne a karamar hukumar Tsafe a matsayin ramuwar gayya kan kisan wani tantirin jagoran 'yan ta'adda da sojoji suka yi
- Farmakin ya jawo an yi arangama mai zafi tsakanin dakarun sojoji da 'yan bindiga, inda aka samu asarar rayuka
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yanma sun yi nasarar fatattakar wasu 'yan bindiga da suka kai musu hari a Zamfara.
Dakarun sojojin sun fatattaki 'yan bindigan ne bayan sun kai musu hari a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun yi arangama da 'yan bindiga
Fafatawar ta jawo an rasa rayukan sojoji biyu tare da raunata 'yan bindiga da dama.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:10 na rana a ranar Talata, a kan hanyar Marabar Kyaware–Unguwar Chida a yankin Tsafe.
An ce harin na ’yan bindigan ya biyo bayan kisan da dakarun sojoji suka yi wa wani shahararren jagoran ’yan ta'adda mai suna Abu A.K tare da wasu daga cikin mabiyansa a wani artabu da suka yi a yankin.
“Sojojin suna kan aikin binciken ababen hawa lokacin da ’yan ta’addan da yawa suka kai musu kwanton bauna."
"Amma dakarun sun nuna jarumta, suka maida martani cikin karfin hali har suka tilasta maharan tserewa dauke da raunukan harbi."
"Abin takaici, sojoji biyu sun rasa rayukansu a yayin musayar wuta, kuma an dauke gawarwakin su zuwa asibiti."
- Wata majiya
Dakarun Sojoji na ci gaba da sintiri
An ce tuni aka tura karin dakaru zuwa yankin tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, inda aka kara tsaurara sintiri domin dawo da zaman lafiya.
Majiyar ta kuma yaba da jarumta da kwarewar dakarun, tana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da hadin gwiwar ayyukan tsaro a fadin jihar Zamfara domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan sojoji
- Ba sauki: Sojojin sama sun samu gagarumar nasara kan 'yan bindiga a Neja
- Dakarun sojoji sun fafata da ƴan bindiga, an gano ƴan China da aka yi garkuwa da su
- 'Yan ta'addan Boko Haram, ISWAP sun yi wa sojoji kwanton bauna, an samu asarar rayuka
An hallaka kwamandan sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun shiryawa dakarun sojojin Najeriya wani mumunan harin kwanton bauna a jihar Borno.
Yan ta'addan sun hallaka kwamandan bataliyar sojoji ta 202 da wasu dakaru biyar da 'yan C-JTF guda uku a harin da ya faru a kauyen Kashimiri, karamar hukumar Bama.
Mummunan harin dai ya auku ne lokacin da jami'an tsaron suke dawowa daga aikin kakkabe sansanonin 'yan ta'adda da ke yankin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


