Asiri Ya Tonu: An Gano Masu Yayata 'Labarin Kisan Kiristoci' a Najeriya

Asiri Ya Tonu: An Gano Masu Yayata 'Labarin Kisan Kiristoci' a Najeriya

  • Wani bincike ya gano yadda kafafen sada zumunta suka taka muhimmiyar rawa wajen ƙara ingiza ikirarin kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya
  • Daga farko daga watan Maris 2025, an gano karuwar ambaton wannan batu mai hadari, wanda ya fara daukar hankalin duniya
  • Binciken ya gano cewa daga ƙasa da  sakonni 5,000 da aka wallafa a tsakanin Maris zuwa Yuli, ya karu zuwa kusan 20,000 a watan Oktoba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Wani bincike da Code for Africa (CFA) da sauran masu nazari suka gudanar ya nuna yadda ake ruruta da ingiza labarin yi wa kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.

Binciken ya gano an yi amfani da kafafen sada zumunta musamman a shafin X wajen ƙara yawan ambaton zargin cewa akwai “kisan kiyashi ga kiristoci a kasar nan.

Kara karanta wannan

"Yara sama da 100,000 na cikin barazana": Manyan Arewa sun waiwayi almajirai

Yan IPOB sun yi amfani da X wajen yada labarin kisan kiristoci
Hoton wasu daga cikin yan kungiyar IPOB Hoto: @therleez
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa an gano a lokacin da Majalisar Dokoki ta Amurka ke sauraron ke tattauna batun a ranar 11–12 Maris, an samu karuwar ambaton lamarin a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka yi amfani da X a Najeriya

Rahoton ya ce daga watan Maris zuwa Yuli, ana magana a kan batun a kasa da sakonni  5,000 da aka wallafa a shafin sada zumunta.

Amma daga Yuli zuwa Agusta ya haura zuwa kusan 10,000; sannan a watan Oktoba ya karu har zuwa kusan 20,000, wanda shi ne mafi yawa a yan shekarun nan.

A wannan lokaci, an kiyasta cewa sakonnin da aka wallafa da suka shafi batun ya kai kusan 165,000 daga 1 Janairu zuwa 1 Oktoba.

Wannan na nufin a rana, ana wallafa sakonni kusan 578 a rana. An kuma ƙididdige cewa wadannan sakonni sun kai ga mutane kimanin  biliyan 2.83.

Bayanai sun nuna cewa magoya bayan kafa kasar Biafra a karkashin IPOB ne su ka fi yatata wannan batu, inda su ke hada wa da fafutukarsu ta balle wa daga Najeriya.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe hatsabibin dan bindiga Abu AK da ya shiga gari cin kasuwa

Gwamnatin Najeriya ta karyata kisan kiristoci

Gwamnatin tarayya ta Najeriya ta bayyana cewa babu wani hujja da ke tabbatar da cewa ana yi wa kiristoci kisan kiyashi.

Gwamntin tarayya ta karyata kisan kiristoci
Hoton Ministan yada labarai, Mohammed Idris Hoto: Mohammed Idris
Source: Twitter

Ministan labarai, Mohammed Idris, ya ce wannan ikirarin “na karya ne, mara tushe, kuma yana iya haifar da rarrabuwar kawunan jama’a.

A yayin da wasu kungiyoyi ke ganin cewa Kiristoci sun fi fuskantar wahala, gwamnatoci da wasu masu nazari suna roƙon a yi aiki da hankali wajen duba lamarin.

"Ana kashe mu": CAN ga gwamnatin Najeriya

A baya, kun ji cewa kungiyar iristocin Najeriya (CAN) ta zargi Fadar Shugaban Ƙasa da yin ƙarya da kokarin sauya gaskiyar rahotannin da ke nuna cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya.

Kungiyar CAN ta ce rahoton fadar shugaban ƙasa ya nuna alamar musanta rahoton, wanda hakan a cewarta ba gaskiya ne, domin a ganinta, ana hada kiristoci ana kashe wa.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Daniel Bwala, ya ce tuhumar CAN ke tuhuma ya dogara ne da labarai daga kafafen waje da kungiyoyin sa‑kai na Turawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng