Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Dan Bindiga, Abu AK da Ya Shiga Gari Cin Kasuwa

Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Dan Bindiga, Abu AK da Ya Shiga Gari Cin Kasuwa

  • Sojojin Najeriya sun hallaka sanannen ɗan ta’adda Abu A.K tare da wasu miyagu a Tsafe, Jihar Zamfara
  • Abu A.K na daga cikin gungun Ado Aleiro, kuma an kama shi bayan ya shigo garin domin cin kasuwar mako
  • Rahoto ya ce sojoji sun kuma kashe wasu ‘yan ta’adda da dama a wani samame da suka kai cikin dajin Tsafe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara – Sojojin Najeriya a karkashin Operation FANSAN YAMMA tare da hadin gwiwar jami’an tsaro sun halaka sanannen ɗan ta’adda mai suna Abu A.K.

Bayan dan ta'addan, sojoji sun yi nasarar kashe wasu daga cikin tawagarsa a karamar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Taswirar jihar Zamfara
Hoton taswirar jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa Abu A.K, wanda ake alakanta shi da fitaccen dan bindiga Ado Aleiro, ya shigo garin Tsafe ne cikin sirri domin cin kasuwa ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

"Yara sama da 100,000 na cikin barazana": Manyan Arewa sun waiwayi almajirai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun ce an gano shi ne bayan an samu bayanan sirri daga wata mace mai suna Halima da ke zaune a unguwar Gabbacin Tsafe, inda daga bisani aka halaka shi yayin artabu da jami’an tsaro.

Yadda aka kashe Abu A.K a Zamfara

Majiyar tsaro ta bayyana cewa bayan samun ingantattun bayanai, dakarun sojoji suka yi gaggawar kai farmaki suka cafke Abu A.K a cikin garin Tsafe.

Bayan an kama shi, sai ya yi yunƙurin tserewa daga hannun jami’an tsaro wanda hakan ya jawo musayar wuta wacce ta kai ga mutuwarsa.

Shugaban 'yan bindiga, Ado Aliero
Ado Aliero da aka kashe yaronsa a Zamfara. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Rahoton ya nuna cewa Abu A.K ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu garkuwa da mutane da ke addabar yankin Tsafe da kewaye, inda ya dade yana aikata kisa, satar shanu da kuma fashi.

Sojoji sun kashe wasu miyagu a Tsafe

A wani ɓangare na aikin, dakarun sojoji da jami’an tsaro sun kai wani kwanton ɓauna da safiyar Litinin a cikin dajin Tsafe, inda suka kashe wasu ‘yan ta’adda da dama.

Kara karanta wannan

DSS ta gano jihohi 2 da 'yan ta'adda ke shirin kai sababbin hare hare

Samamen ya gudana ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe, kuma jami’an tsaro sun bayyana shi a matsayin babbar nasara a yaƙin da ake yi da ‘yan ta’adda a yankin.

A cewar majiyoyi, an samu makamai ciki har da bindigogi daga hannun miyagun da aka kashe, yayin da wasu suka tsere cikin daji.

An kai gawar Abu A.K sansanin Magazu

Bayan kammala aikin, an kwashi gawar Abu A.K zuwa sansanin Magazu, wanda yake ɗaya daga cikin sansanonin rundunar sojoji a karamar hukumar Tsafe domin cikakken bincike.

Majiyoyi sun ce jami’an tsaro sun tabbatar da cewa shi ne mutumin da ke da alhakin kisan ma’aikatan kamfanin Setraco Construction uku mako biyu da suka gabata.

Turji ya saki sama da mutum 100

A wani rahoton, kun ji cewa an fara sabon shirin neman sulhu da shugaban 'yan ta'adda a Najeriya, Bello Turji.

Rahotanni sun bayyana cewa yayin da ke magana kan sulhun, Turji ya saki mutane sama da 100 da ya yi garkuwa da su.

Masu shiga tsakani sun bayyana cewa za su yi kokarin ganin cewa dan ta'addan bai cigaba da daukan makami ba bayan sulhun.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng