Ranar Manzon Allah: Malami Ya Nuna Damuwa game da Bikin, Ya Roki Abba Kabir
- Babban malamin Musulunci daga Kaduna, Sheikh Ibrahim Aliyu, ya roki Gwamna Abba Kabir Yusuf kan gangamin Yaumul Rasul
- Malamin ya bayyana damuwarsa cewa taron yan dariku na iya jawo rikici kamar yadda aka gani wajen wasu taruka baya
- Sheikh Ibrahim ya ce “Yaumul Rasul” bidi’a ce, yana kuma rokon gwamnatin Kano ta dauki mataki don kare zaman lafiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Babban malamin Musulunci daga jihar Kaduna ya sake tsoma baki kan abin da ke faruwa a jihar Kano.
Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya yi gaggawar taka wa yan dariku birki a jihar da suke shirin yin gangami.

Source: Facebook
Ranar Manzon Allah: Malami ya roki Abba Kabir
Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Abdullahin Gwandu TV ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan
Gwamna ya bi sahun Peter Mbah ya koma jam'iyyar APC mai mulki? Gaskiya ta bayyana
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A bidiyon, malamin addinin ya nuna damuwa kan shirin yan dariku na gudanar da gangami da suka kira 'Yaumul Rasul' wato ranar Manzon Allah.
Ya ce:
"Akwai abin da muka gani ana yunkurin yi duka saboda matsalar Malam Lawan Triumph, an samu wasu yan darika za su yi tattaki na mutum kaza.
"Wai wata sabuwar rana wai yaumur rasul, wata sabuwar bidi'a ce da aka fito da ita wato ranar Manzon Allah.
"Mu na kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayinka na shugaba ba komai za ka yarda da shi a jiharka ba, mutane su yi gangami a zo a yi karan batta ba abu ba ne wanda ya dace."

Source: Facebook
Matsalar da aka hango kan ranar Manzon Allah
Shehin malamin ya ce wannan taro zai iya jawo cikas a cikin al'umma duba da abin da ya faru a lokacin tattakin takutaha a Kano.
Ya kara da cewa:
"Idan wani taro da aka saba yi wannan ba matsala ba ne, amma wasu mutane su ware rana daya su ce wai za su yi yaumul Rasul.
"Mun ga dai abin da ya faru a ranar takutaha, wasu yan ta'adda daga cikin yan dariku suka kai wa malaminmu hari, da kyar ya sha da rayuwarsa, aka kona masallaci da litattafansa aka kona dakin karatu.
"Wannan ma taron gangamin da za a yi ba mu san dalilinsa ba, abin da muke gudu shi ne tsinkewar fitina a cikin al'umma, idan magana na gaban gwamnati, to wani ya fito ya ce zai yi wani abu neman tsokana ne."
Daga karshe, malamin ya roki gwamnan ya yi abin da ya dace domin daukar mataki saboda abu ne wanda Allah da Manzonsa ba su ce a yi ba.
Malamin darika ya bukaci mukabala da Triumph
A baya, mun ba ku labarin cewa Sheikh Uwais Limanci kuma dan Darikar Tijjaniyya a Kano, ya ce bai yarda da hujjojin Malam Lawan Abubakar Shuaibu Tirumph ba.
Malamin ya nemi a gudanar da mukabala a bainar jama’a domin a tabbatar da gaskiyar hujjojin da Sheikh Triumph ya gabatar.
Majalisar shura ta Tijjaniyya ta yi kira ga gwamnati da ta kafa dokar wa’azi da za ta hana batanci tsakanin malaman jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

