'Yan Bindiga Sun Bude Wa Mota Wuta, Sun Yi Awon gaba da Ma'aikatan INEC a Kogi

'Yan Bindiga Sun Bude Wa Mota Wuta, Sun Yi Awon gaba da Ma'aikatan INEC a Kogi

  • Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun jefa jama'a a cikin tashin hankali bayan sun tare wadansu ma’aikatan INEC a jihar Kogi
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa mayakan dauke da makama sun sace mata uku daga cikin matafiya a hanyarsu ta zuwa jihar Anambra
  • Sun nufi jihar Anambra ne domin gudanar da zabe, sai dai yan ta'addan sun tare su a iyakar jihohin Kogi da Binuwai, suka yi awon gaba da su

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kogi – Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace ma’aikatan hukumar zabe ta kasa wato INEC guda uku da wasu mutane a kusa da garin Aloma,

Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin a faru a karamar hukumar Ofu a jihar Kogi wanda ke iyaka da jihar Binuwai.

Kara karanta wannan

Kotu ta fadi dalilin dage zaman shari'ar kwamandojin 'Yan ta'addan Ansaru

Yan bindiga sun kai hari Kogi
Wwadu daga cikin sojojin Najeriya Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa wadanda aka sace su sun hada da Chinenye Oji, Adamaka Anih, da Catherine Temaugee — mata ne gaba dayansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindiga sun sace ma'aikatan INEC

Daily Post ta ruwaito cewa duka matan da aka sace, ma'aikatan hukumar INEC ne daga hedkwata da ke babban birnin tarayya Abuja.

An ce suna cikin tafiya ne zuwa jihar Anambra domin shirye-shiryen zaben gwamna da za a gudanar a ranar 8 ga Nuwamba, 2025.

Wani dan uwa ga daya daga cikin wadanda aka sace, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce an sace matan a motar haya kirar Sienna da suka dauka daga Utako, Abuja da safiyar Talata.

A cewarsa:

“Sun tashi ne da safe daga Abuja zuwa Anambra don shirye-shiryen zabe, kamar buga rajistar masu kada kuri’a da sauran kayan aiki.”

'Yan bindiga sun saki wasu mutane

Masu garkuwar sun tare motar, suka bude wuta suka tarwatsa gilashin motar, duk da haka ba a ji rauni ba, amma sun tilasta motar ta tsaya kuma suka kwashe fasinjojin zuwa cikin daji.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mutane da yawa sun mutu da wata tanka ta yi bindiga a Najeriya

An ce sun sako wata tsohuwa da ke cikin motar saboda tana da matsalar kafa, sannan suka bar direban motar don ya kai matar zuwa garin da ya fi kusa da su.

An sace ma'aikatan INEC a Kogi
Taswirar jihar Kogi, inda aka sace ma'aikatan INEC Hoto: Legit.ng
Source: Original

Har zuwa yanzu dai babu labarin inda aka kai wadanda aka sace, kuma jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, William Aya, ya ce:

“Ban samu rahoton hakan ba tukuna. Zan tuntubi DPO na yankin domin jin me ya faru.”

Ita ma hukumar INEC da aka sace ma'aikatanta ba ta komai ba a kan lamarin zuwa lokacin rubuta wannan labari.

'Yan bindiga suna shirin kai hari

A baya, mun ruwaito cewa hukumar tsaro ta DSS ta fallasa cewa ta samu sahihan rahotanni da ke nuna cewa akwai jihohi biyu da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ke shirin kai hare‑hare.

A cewar rahotannin, yanzu haka miyagun mutanen sun fara tattara makamai, mayaka, da kuma zaɓen wuraren da za a yi amfani da su wajen kai wa jama'a farmaki haka kurum.

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta roki al’umma da su yi taka‑tsantsan da kuma bayar da bayanai ga jami’an tsaro idan sun lura da wani al’amari da ya saba da abin da suka saba gani.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng