Bayan Mutuwar Mai Martaba Sarki, Uba Sani Ya Nada Sabon Basarake a Kaduna
- Gwamnatin Kaduna ta amince da nadin sabon basarake bayan rasuwar Mai Martaba Yohanna Sidi Kukah a Disambar 2024
- Gwamna Uba Sani ya nada Bature Sunday Likoro a matsayin Sarkin yankin, tare da taya shi murna da fatan nasara da jagoranci
- Haka kuma, gwamnan ya amince da aiwatar da kashi 70 na tsarin albashi na 2024 ga malamai da ma’aikatan manyan makarantu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Gwamnatin Jihar Kaduna ta amince da nadin sabon Sarki bayan rasuwar tsohon basaraken, Yohanna Sidi Kukah a jihar.
Gwamna Uba Sani ya nada Bature Sunday Likoro a matsayin sabon Agwom Kamuru inda ya yi masa addu'ar jagoranci nagari.

Source: Twitter
Uba Sani ya nada sabon Sarki a Kaduna
Hakan na cikin wani rubutu da hadimin gwamnan a bangaren sadarwar zamani, Abdallah Yunus Abdallah ya wallafa a shafin X a jiya Talata 21 ga watan Oktobar 2025.
Nadin sabon Sarkin na zuwa ne bayan rasuwar tsohon Sarkin yankin, Mai Martaba Yohanna Sidi Kukah, a ranar 18 ga Disamba, 2024.
Sanarwar wanda Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi, Sadiq Mamman Lagos, ya sanyawa hannu ta ce nadin zai fara aiki nan take.
Kwamishinan ya ce Gwamna Uba Sani ya tabbatar da nadin Likoro a matsayin Sarki mai daraja ta Uku.
An bayyana cewa sabon Sarkin, wanda aka haifa a ranar 15 ga Agusta, 1958, yana da digirin HND a harkar kasuwanci daga Kwalejin Fasaha a Kaduna.
Har ila yau, kuma yana da kima da tasiri a al’ummarsa saboda ayyukan cigaban da ya gudanar a baya.
Duk da cewa an ta ce nadin ya fara aiki nan take, sanarwar ta ce za a sanar da ranar bikin nadin sarauta da mika sandar mulki daga baya.
Kwamishinan ya kara da cewa Gwamna Uba Sani ya taya sabon Sarkin murna bisa samun kujerar tare da yi masa fatan nasara da shiriya daga Allah.

Source: Facebook
Abin alheri da Uba ya yi ga ma'aikata
A wani bangare na sanarwar, Gwamna Uba Sani ya amince da aiwatar da 70% na tsarin albashi na CONPCASS/CONTEDISS na 2024 ga ma’aikatan makarantun gaba da sakandare na jihar Kaduna.
Wannan mataki ya kawo karshen yajin aikin da kungiyoyin malamai suka fara a ranar 30 ga Satumba, 2025, bayan taron da aka gudanar tsakaninsu da gwamnati a gidan gwamnati Kaduna.
Kungiyoyin sun yaba da matakin, suna cewa hakan na nuna gaskiya da jajircewar gwamnati wajen kare ilimi da walwalar ma’aikata.
Gwamna ya kuma amince da shekaru 65 a matsayin shekarun ritaya da kuma shekaru 40 na aiki ga ma’aikatan da ba malamai ba.
Uba Sani ya yiwa Tinubu alkawari a 2027
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya halarci wani babban gangamin da aka shirya na jam'iyyar APC mai mulki.
A yayin gangamin, Gwamna Uba Sani ya karbi mambobin jam'iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC mai mulkin Najeriya.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa yanzu babu sauran wata adawa a jihar, kuma jam'iyyar APC za ta samu mafi yawan kuri'u a zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


