Kano: Kwankwaso Ya Kafa Tubalin Gina Jami'ar Likitanci a Gida, Ya Godewa Abba

Kano: Kwankwaso Ya Kafa Tubalin Gina Jami'ar Likitanci a Gida, Ya Godewa Abba

  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi murnar bikin zagayowar ranar haihuwarsa da abubuwan alheri
  • Kwankwaso ya kafa tubalin gina jami’ar likitanci a Kwankwaso da ke Madobi, domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa a jiya
  • Jagoran na Kwankwasiyya ya ce makarantar ta fara aiki 2019, ta yaye da dalibai 400, kuma yanzu 400 na ci gaba da karatu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Madobi, Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

A yayin bikin murnar, Rabiu Kwankwaso ya kaddamar da ginin jami’ar likitanci a garin Kwankwaso, karamar hukumar Madobi.

Kwankwaso ya gina tubalin gina jami'arsa ta likitanci a Kano
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayin kaddamar da jami'ar a Kano. Hoto: Gida Gida TV.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da shafin Gida Gida TV ya wallafa a Facebook a jiya Talata 22 ga watan Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya nuna yatsa ga kasashen Yamma kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya kafa tubalin gina jami'ar likitanci

Wannan aiki na cikin shirye-shiryen bikin cika shekara 69 da haihuwarsa, inda aka gudanar da bikin a kwalejin koyon aikin jinya ta Nafisatu.

A wajen taron, Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa wannan mataki babbar nasara ce a kokarinsa na fadada ilimin kiwon lafiya, musamman ga matasa mata a yankin.

Ya ce:

“Makarantar ta fara aiki a 2019, kuma zuwa yanzu dalibai 400 sun kammala karatu, yayin da wasu 400 ke ci gaba da karatu.”

Ya jaddada cewa kwalejin ce ta farko a Najeriya mai zaman kanta da ke koyar da jinya da ungozoma, kuma dukkan daliban mata ne.

“Sakamakon da ake samu a karatun ya karfafa mana gwiwa muka dauki mataki na gaba, shi ne kafa jami’ar likitanci."

- Rabi'u Musa Kwankwaso

Kwankwaso ya dauko niyyar inganta harkar lafiya a Kano
Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Godiya da Kwankwaso ya yi ga Abba Kabir

Kwankwaso ya gode wa Gwamnatin Abba Kabir bisa taimakon bayar wajen horas da ungozomai na al’umma, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

DSS ta gano jihohi 2 da 'yan ta'adda ke shirin kai sababbin hare hare

Ya ce sabon tsarin zai taimaka wajen karfafa ma’aikatan lafiya da rage karancin likitoci da ungozomai a kasa.

Kwankwaso, wanda ya kafa makarantar a matsayin wani ɓangare na zuba jarinsa a fannin ilimi da ci gaban ɗan Adam, ya ce sabunta cibiyar wani yunkuri ne na ƙara damar da mata matasa za su samu don yin karatun likitanci da sauran fannoni na lafiya.

Ya ƙara da cewa:

“Za mu je wurin da muke shirin ɗaga matsayin wannan cibiyar daga Kwalejin Koyon Kimiyyar Lafiya zuwa Jami’ar Likitanci."

Shugaban majalisar kwalejin, Farfesa Saleh Ngaski Garba, ya yaba wa Kwankwaso bisa hangen nesa da jin kai.

Ya ce kwalejin ta fitar da ungozomai da jinya 416 tun kafuwarta, kuma sabuwar jami’ar za ta kara damar karatun matasa masu karamin karfi a fannin lafiya.

Shekaru 69: Tinubu ya taya Kwankwaso murna

Kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa har yanzu tsohon gwamnan Kano kuma jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso abokinsa ne.

Tinubu ya aika da sakon taya murna da fatan alheri ga Kwankwaso yayin da ya cika shekara 69 a ranar 21 ga watan Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

Kana naka: Darakta ta mutu a hatsarin mota kwana 4 kafin ritaya a aikin gwamnati

Shugaban ya tuna irin gudummuwar da Kwankwaso ya bayar tun lokacin da suke tare a Majalisa har kawo yanzu da ya koma NNPP.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.