Majalisar Dattawa ba Ta Kunyata Tinubu ba, Ta Amince da Nadin Sabon Shugaban NPC
- Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Dr. Aminu Yusuf daga jihar Neja a matsayin sabon shugaban hukumar NPC
- Majalisar ta kuma amince da nadin Joseph Haruna Kigbu da Tonga Betara Bularafa a matsayin kwamishinoni a NPC
- Rahoton kwamitin majalisar ya tabbatar cewa ba a samu wani korafi ko zargin aikata laifi kan wadanda aka nada ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin Dr. Aminu Yusuf daga jihar Neja a matsayin sabon shugaban hukumar kidayar jama’a ta kasa (NPC), tare da kwamishinoni biyu.
Wannan tabbaci ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin majalisar kan shaidar dan kasa da kidaya, wanda Sanata Victor Umeh, dan majalisar Anambra ta Tsakiya, ya jagoranta.

Source: Twitter
Kwamitin majalisa ya tantance shugaban NPC
A cewar Sanata Umeh, wadanda aka nada sun bayyana gaban kwamitin a ranar 14 ga Oktoba, 2025, domin tantance su bisa cancanta da ƙwarewa, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Kwamitin bai karɓi wani korafi ba daga kowace hukuma ko mutum a kan wadanda aka nada. Sun kuma nuna azamarsu ta aiwatar da aikin da aka nada su yadda ya kamata."
- Sanata Victor Umeh.
Sanatan ya bayyana cewa, sai da kwamitin ya karbi dukkan takardu da suka haɗa da CV, rahoton hukumar da'ar ma'aikata (CCB), rahoton ‘yan sanda da DSS, kafin fara tantancewar.
A yayin tantancewar, Dr. Aminu Yusuf da kwamishinonin da aka nada sun gabatar da bayanai game da yadda suke sa ran kawo ci gaba da kuma yadda za su inganta aikin hukumar NPC.
Sanata Umeh ya ce:
“Kwamitin ya duba takardunsu, ilimi, da kwarewa, sannan ya gamsu da cancanta da dacewarsu da mukaman da aka nada su.”
Majalisar ta amince da nadin shugaban NPC
Sanata Tony Nwoye daga Anambra ta Arewa ne ya goyi bayan rahoton kwamitin, kafin majalisar ta shiga zaman kwamiti baki ɗaya don duba rahoton.

Kara karanta wannan
Ta tabbata, sojojin Najeriya sun kama hatsabibin ɗan ta'adda da aka jima ana nema
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bukaci a kada kuri'ar baki kan wannan nadin, inda ‘yan majalisa suka amince gaba ɗaya.
“An amince da nadin Aminu Yusuf daga Neja a matsayin Shugaban NPC, da Joseph Haruna Kigbu daga Nasarawa, da Tonga Betara Bularafa daga Yobe a matsayin kwamishinoni.”
- Sanata Godswill Akpabio.

Source: Twitter
Nadin ya samu amincewar majalisar koli
A baya, Majalisar Koli ta Ƙasa ce ta amince da nadin Dr. Aminu Yusuf bisa shawarwarin Shugaba Bola Tinubu, inji rahoton jaridar Punch.
Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron Majalisar Koli da aka gudanar a fadar shugaban kasa a ranar 9 ga Oktoba, 2025.
“Majalisar Koli ta amince da nadin shugaban hukumar kidayar jama’a, kuma mutumin da aka zaɓa bisa shawarwarin shugaban kasa shi ne Dr. Aminu Yusuf daga jihar Neja.”
- Gwamna Uba Sani.
Tinubu ya gabatar da bukatu ga majalisa
Tun da fari, mun ruwaito cewa, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da bukatu biyar ga majalisar dattawa, ciki har da nadin shugaban NPC.
Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya karanta wasikar Tinubu, inda ya nemi a tantance tare da amincewa da nadin Dr. Aminu Yusuf a matsayin shugaban NPC.
Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya mika wannan batun zuwa ga kwamitin shaidar dan kasa da kidayar jama’a don ba da rahoto cikin mako guda.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

