Hukumar Kidaya ta Sanar da Ranar Fara Kidaya a Najeriya a 2023

Hukumar Kidaya ta Sanar da Ranar Fara Kidaya a Najeriya a 2023

  • Hukumar Kidaya ta kasa ta sanar da cewa za a fara aikin kirga jama’a da gidaje a Najeriya a ranar 29 na watan Maris zuwa 1 ga watan Afirilun 2023
  • Shugaban hukumar, Nasir Kwarra, ya sanar da cewa jami’an za su yi amfani da kayan aiki na fasaha wurin tabbatar da sun yi aikin da ya dace
  • Ya sanar da manema labaran gidan gwamnati cewa, har da bakin haure za a kirga matukar suna kasar yayin da ake kidayar

FCT, Abuja - Hukumar kula da kidaya ta kasa, NPC, ta saka ranar 29 na watan Maris zuwa ranar 1 ga watan Afirilun 2023 don kidayar jama’a da gidaje a Najeriya.

Da dumi
Hukumar Kidaya ta Sanar da Ranar Fara Kidaya a Najeriya a 2023
Asali: Original

Nasir Kwara, shugaban NPC, ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labaran gidan gwamnati bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

NDLEA Tayi Abin da Ba a Taba Yi ba a Tsawon Shekara 33 a Karkashin Buba Marwa

“Nan da ranar 29 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afirilu, ma’aikatansu za su fada aikin kidaya.”

- Yace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwarra ya kara da cewa, Za a yi amfani da kayan aiki na fasaha da za su iya duba gidaje har su nada bayanan inda suke da sauransu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Shugaban NPC, wanda yace hukumarsa za ta tabbatar da cewa tayi aikin gaskiya, ya kara da cewa har da bakin haure za a kirga matukar suna kasar nan yayin da ake kidayar.

Kwarra yace:

"Daga ranar 29 na watan Maris zuwa 2 ga watan Afirilu, ma'aikatanmu za su fita aikin kirga jama'a. Wannan kidayar za t sha banban da sauran da aka yi a baya.
"Bayanin da yadda za a yi shi kusan iri daya ne amma wannan za mu yi amfani da fasaha sosai ta yadda babu wanda zai iya canza yaan. Babu wanda za a kirga sama da sau daya.

Kara karanta wannan

Toh fa: Gwamna Wike ya fadi dan takarar da zai marawa baya a zaben 2023 mai zuwa

"Za mu ziyarci gidaje domin ganawa kai tsaye da jama'a, daukar bayanai. A baya idan kana aiki da kan ka yana da yawa, amma wannan za mu samu taimakon fasaha kuma na yarda za a yi sauri saboda mun samar da bayanan kananan hukumomi har zuwa matakin gunduma."

Kwarra yace an kammala rarrabe lambobin yankuna tuni, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Yace an bude shafin yanar gizo na daukar ma'aikata da ma'aikatan wucin-gadi domin aiki inda ya kara da cewa wadanda aka daukan za a ajiye su ne a yankunansu.

Shugaban NPC din yayin bayani kan tsaro a wasu sassan kasar nan, ya bayyana fatansa na cewa za a yi kidayar lafiya kalau a irin yankunan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel