Gwamna Abba Ya Yi Magana kan Munafukai Masu Son Raba Shi da Kwankwaso
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya taya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 69 da haihuwa
- Abba ya bayyana Sanata Kwankwaso a matsayin gwarzon da ya sadaukar da rayuwarsa wajen taimakon al’umma
- Mai girma Gwamnan ya kuma bukaci 'yan Kwankwasiyya da su ci gaba da hada kai da ba munafukai kunya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana farin cikinsa yayin da yake taya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso murnar cika shekara 69.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya bayyana Kwankwaso a matsayin gwarzon da Allah ya yi wa baiwa ta musamman.

Source: Facebook
A bidiyon da Kwankwasiyya Reporters suka wallafa a Facebook, gwamnan ya ce ranar haihuwar jagoran tafiyar Kwankwasiyya rana ce ta tarihi domin tunawa da irin gudunmuwar da ya bayar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma yi kira ga dukkan mabiya tafiyar Kwankwasiyya da su ci gaba da hadin kai da aiki tukuru domin tabbatar da ci gaba da dorewar nasarorin da tafiyar ta assasa a Kano.
Kwankwaso dan baiwa ne inji Abba Kabir
Gwamna Abba ya ce Sanata Rabiu Musa Kwankwaso mutum ne mai baiwa da tausayi wanda ya dade yana bayar da gudunmawa ga al’umma tun yana da kananan shekaru.
Ya bayyana cewa tun lokacin da Kwankwaso yake karatu a sakandare har zuwa lokacin da ya zama dan majalisa, yana tallafawa jama’a domin ya kawo cigaban al’umma.
Ya kara da cewa:
“Allah ya gama mana komai da ya ba mu Kwankwaso, amma mutane da yawa sun kasa gane waye shi.”
Abba: 'Mutane ba su san Kwankwaso ba'
Gwamnan ya ce irin jajircewar Kwankwaso wajen karfafa ilimi da taimakon marayu abin koyi ne ga shugabanni a kowane mataki.
Abba ya ce Allah ya musu komai da ya ba su Kwankwaso, duk da haka ya ce mutane da yawa sun kasa gane waye shi.

Kara karanta wannan
"Allah zai tona asirinsu": Tsohon sakataren gwamnatin Kano ya budewa Kwankwaso wuta
Ya kuma yi fatan Allah Ya kara wa jagoran tafiyar Kwankwasiyya lafiya da tsawon rai domin ya ci gaba da jagorantar al’umma bisa tafarkin gaskiya da adalci.
Abba ya yi magana kan munafukai a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci mabiya tafiyar Kwankwasiyya da su ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya domin tabbatar da ci gaban Kano da kare darajar tafiyar.
A cewarsa:
“Ina so in gayawa al’umma, musamman ‘yan Kwankwasiyya, cewa tafiyarmu tana nan daram.
"Muna tare da Sanata Rabiu Kwankwaso, kuma duk wasu munafukai ko na gida ko na waje, karyarsu ta sha karya.”
Ya kara da cewa taron da suka gudanar shi ne karo na bakwai, yana mai fatan Allah ya sa a ci gaba da gudanar da irin wadannan taruka masu nuni da kauna da hadin kai a jihar Kano.

Source: Facebook
Gwamna Abba ya godewa malamai, farfesoshi, mata da maza da suka halarci taron domin nuna kauna da goyon baya ga tafiyar Kwankwasiyya.
Ado Doguwa ya yabi Rabiu Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa dan majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya yaba wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Hon. Doguwa ya yi magana ne yayin da Kwankwaso ya halarci wani zama na majalisar wakilai na bankwana da tsohon shugaban majalisar.
'Dan majalisar ya tuna lokacin da Rabiu Kwankwaso ya tallafa masa a lokacin da ya ke mataimakin shugaban majalisar wakilai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

