DSS Ta Gano Jihohi 2 da 'Yan Ta'adda Ke Shirin Kai Sababbin Hare Hare
- Hukumar DSS ta fitar da takardar sirri da ke nuna cewa mayakan ISWAP na shirin kai sababbin hare-hare a Ondo da Kogi
- Takardar ta lissafo Owo, Eriti Akoko da Oyin Akoko a matsayin yankunan da ake kyautata zaton za a kai wa hare-haren
- Rundunar ‘yan sanda ta gudanar da babban taron tsaro da shugabannin al’umma domin hana faruwar kowane rikici
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar DSS ta fitar da gargadi mai matuƙar muhimmanci kan shirin kungiyar ISWAP na kai hari a wasu garuruwan jihohin Ondo da Kogi.
Wannan gargadin na kunshe ne a cikin takardar sirri mai kwanan wata 20 ga Oktoba, 2025, wacce aka aike wa kwamandan 32 Artillery Brigade na rundunar sojin Najeriya da ke Owena Cantonment, Akure.

Source: Facebook
Takardar wacce daraktan tsaro na DSS a jihar Ondo, Hi Kana, ya sanya wa hannu, ta nuna cewa an samu sahihin bayanan sirri cewa ‘yan ta’addan na shirin kai hare-hare, inji rahoton The Nation.
'Yan ta'adda za su kai hari jihohi 2
A cikin bayanin, DSS ta lissafo Eriti Akoko da Oyin Akoko a Akoko ta Arewa maso Yamma, tare da Owo a karamar hukumar Owo, a matsayin yankunan da ke cikin haɗarin kai wa hari.
Hukumar ta ce ‘yan ta’addan sun fara gudanar da leƙen asiri a wadannan yankuna, tana kuma roƙon jami’an tsaro da su ƙara matakan tsaro domin hana asarar rayuka da dukiyoyi.
“An tabbatar da cewa ‘yan ISWAP na shirin kai hare-hare nan ba da jimawa ba. Ya zama dole a ƙara tsaro a dukkan yankunan da aka ambata,” in ji takardar DSS.
Wannan gargadi na zuwa shekaru uku bayan mummunan harin da aka kai Cocin Katolika ta St. Francis, Owo, a watan Yunin 2022, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 40.
‘Yan sanda sun kira taro kan hare-haren
Biyo bayan wannan gargadi, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ondo, CP Adebowale Lawal, ya gudanar da babban taron tsaro a Ikare Akoko tare da shugabannin al’umma da jami’an tsaro.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, Ayanlade Olayinka, ya bayyana cewa taron ya kasance wani ɓangare na kokarin hana rikice-rikice da tabbatar da tsaro bisa shirin IGP Kayode Egbetokun.
Taron ya haɗa da sarakunan gargajiya, kungiyar masu noma, NURTW, kungiyar masu babura (Okada), da wakilan Fulani da Igbo, da kuma 'yan sa kai da PCRC, a cewar Vanguard.

Source: Twitter
Haɗin kai tsakanin al’umma da jami’an tsaro
Mahalarta taron sun yabawa kokarin ‘yan sanda wajen tabbatar da zaman lafiya, inda suka yi alkawarin bayar da bayanai masu inganci ga jami’an tsaro.
Sarakunan gargajiya da shugabannin Fulani sun jaddada muhimmancin tsare iyakokin jihohi da ke haɗa Ondo, Ekiti, da Kogi domin dakile barazanar ‘yan ta’adda.
Kwamishinan ‘yan sanda, CP Lawal, ya bayyana cewa kofarsa a buɗe take don sauraron shawarwari, inda ya raba lambar wayarsa kai tsaye domin sauƙaƙe isar da bayanai.
ISWAP ta kashe shugaba a Borno
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ISWAP ta kara yin ta'addancin da ta saba yi a jihar Borno duk da kokarin ganin bayan miyagun da sojoji ke yi.
Mayakan ISWAP sun je har gida sun yi awon gaba da wani shugaban kungiyar mafarauta, kafin daga bisani suka kashe shi har lahira.
Harin ya kara fito da matsalar rashin tsaron da aka dade ana fama da ita, musamman hare-haren ISWAP da Boko Haram, da suka jawo asarar rayuka a Borno.
Asali: Legit.ng


