Ta Tabbata, Gwamna Bala Ya Rattaba Hannu kan Dokar Kafa Sababbin Masarautu 13

Ta Tabbata, Gwamna Bala Ya Rattaba Hannu kan Dokar Kafa Sababbin Masarautu 13

  • Gwamna Bala Mohammed ya sanya hannu kan dokar kaView on sitefa sababbin masarautu 13 da hakimai 111 a fadin jihar Bauchi
  • Ya kuma soke tsohuwar masarautar Sayawa, ya kafa masarautar Zaar da hedkwatarta a Mhrim Namchi, Tafawa Balewa
  • Gwamnan ya gargadi masu siyasantar da doka, ya kuma rattaba hannu kan dokar fansho da karin kasafin kudi na 2025

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya sanya hannu kan dokar nadi da sauke sarakuna, wacce ta kafa sababbin masarautu 13 da akalla hakimai 111 a fadin jihar.

Haka kuma, gwamnan ya rattaba hannu kan dokar soke masarautar Sayawa, tare da kafa masarautar Zaar mai hedkwata a Mhrim Namchi, karamar hukumar Tafawa Balewa.

Gwamna Bala Mohammed ya sanya hannu kan dokar kirkirar sababbin masarautu 13
Hoton gwamnan Bauchi, Bala Mohammed yana sanya hannu kan dokar kafa sababbin masarautu 13. Hoto: Mukhtar Gidado
Source: Facebook

Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Bauchi, Mukhtar Gidado ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Kotun Koli ta shirya raba gardama kan dokar ta bacin da Tinubu ya sa a Rivers

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce wannan mataki zai inganta tsarin masarautu, ya kara hadin kai, da samar da zaman lafiya tsakanin kabilu da al’ummomi a jihar Bauchi.

Bauchi: Cikakkun sunayen sabbbin masarautu

Sabbin masarautun da gwamnan ya amince da su da hedkwatocinsu sune kamar haka:

  1. Masarautar Burra – Hedkwata a Burra
  2. Masarautar Duguri – Hedkwata a Yuli
  3. Masarautar Dambam – Hedkwata a Dambam
  4. Masarautar Bununu – Hedkwata a Bununu
  5. Masarautar Lere – Hedkwata a Lere
  6. Masarautar Darazo – Hedkwata a Darazo
  7. Masarautar Jama’a – Hedkwata a Nabardo
  8. Masarautar Lame – Hedkwata a Gumau
  9. Masarautar Toro – Hedkwata a Toro
  10. Masarautar Ari – Hedkwata a Gadar Maiwa
  11. Masarautar Warji – Hedkwata a Katangar Warji
  12. Masarautar Giade – Hedkwata a Giade
  13. Masarautar Gamawa – Hedkwata a Gamawa

Haka kuma, an kafa hedkwatar masarautar Zaar (masarautar Sayawa) a Mhrim Namchi, karamar hukumar Tafawa Balewa.

Gwamna ya gargadi masu siyasantar da doka

Da yake jawabi a fadar gwamnati, Gwamna Bala ya gargadi duk masu kokarin siyasantar da sababbin dokokin da aka kafa, yana mai cewa gwamnati ba za ta lamunta ba.

Kara karanta wannan

MCAN: 'Yan NYSC Musulmi sun yi taron Arewa maso Gabas a Gombe

“Wannan gwamnati ba za ta yarda da duk wani yunkuri na kawo rabuwar kai, yada jita-jita ko tada rikici ba,” in ji shi.

Ya umarci hukumomin tsaro da su dauki mataki kai tsaye kan duk wanda ya karya doka ko ya yi yunkurin tayar da tarzoma.

Gwamnan ya kuma gargadi duk wani jami’in gwamnati ko hakimi da ya yi wani abu da zai ci karo da manufar wannan sauyi.

Gwamna Bala ya gargadi masu siyasantar da dokoki a Bauchi.
Gwamna Bala Mohammed da kakakin majalisar Bauchi lokacin sanya hannu kan sabuwar dokar masarautu. Hoto: Mukhtar Gidado
Source: Facebook

Majalisar Bauchi ta fadi dalilan kafa dokar

Kakakin majalisar dokokin Bauchi, Abubakar Y. Suleiman, ya ce sabuwar dokar ta samo asali ne daga tattaunawa mai zurfi da al’umma da sarakunan gargajiya.

Ya ce wannan doka tana nuna yadda gwamnatin jihar ke neman inganta shugabanci mai nagarta da karfafa dimokuradiyya ta hanyar shigar da jama’a a ciki.

Bala Mohammed ya kuma rattaba hannu kan dokar hadakar fanshon kananan hukumomi, inda ya yi alkawarin biyan bashin fansho da gratuti na tsofaffin ma’aikata.

Haka kuma ya amince da kudirin karin kasafin kudi na 2025, domin tallafa wa ci gaban ayyukan gine-gine da shirye-shiryen raya kasa na gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Ta tabbata, sojojin Najeriya sun kama hatsabibin ɗan ta'adda da aka jima ana nema

Fulani sun bijirewa gwamnan Bauchi

A wani labari, mun ruwaito cewa, Fulani sun ƙi amincewa da yunkurin Gwamna Bala Mohammed na ƙirƙirar sababbin masarautu a jihar Bauchi.

Kungiyar Fulani ta Daddo Pulaku ta ce za su ci gaba da biyayya ga masarautu shida da ake da su a Bauchi, don zaman lafiya da haɗin kai.

Daddo Pulaku ta gargadi gwamnatin Bauchi kan cewa kirkirar sababbin masarautu zai iya kawo ƙabilanci da kuma haifar da tashin hankali.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com