Ana Fargabar Mutane da Yawa Sun Mutu da Wata Tanka Ta Yi Bindiga a Najeriya
- Wata tanka makare da mai ta fashe a kan titin Agaie zuwa Bida a jihar Neja da yammacin yau Talata, 21 ga watan Oktoba, 2025
- Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadurra ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce har yanzu ba a tantance yawan wadanda suka mutu ba
- Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin tankar ya haifar da cunkoson ababen hawa a titin, wanda ke tara matafiya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Ana fargabar mutane da dama sun mutu a wani mummunan fashewar tankar mai da ta faru a yankin Essa, kan hanyar Agaie–Bida da ke jihar Neja a yammacin ranar Talata.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya haddasa cunkoson ababen hawa mai tsanani a babbar hanyar, inda motoci suka makale na sa’o’i da dama.

Source: Original
Shugabar hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) a jihar Neja, Hajiya Aishatu Sa’adu, ta tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
FRSC ta tabbatar da fashewar tanka a Neja
Sai dai Hajiya Aishatu ta ce ba a iya tantance adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata ba har zuwa lokacin da take magana da manema labarai.
Da take hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), Aishatu Sa’adu ta bayyana cewa jami’anta sun isa wajen da lamarin ya faru don gudanar da aikin ceto da kashe gobara.
A kalamanta, shugabar FRSC ta Neja ta ce:
“Lamarin ya haddasa cunkoson ababen hawa mai tsanani, musamman saboda lalacewar titin. Wannan rashin kyau na hanya ya jinkirta zuwan motocin ceto da na kashe gobara.”
Hadurra na yawan faruwa a titin Bida
Titin da ya taso daga Bida ya ratsa ta Agaie har zuwa Lapai ya shahara musamman a kafafen watsa labarai saboda hadurran tankokin mai da ke faruwa a kai a kai.
A bara, mutane 48 sun mutu a wata fashewar tanka a wannan hanya, bayan da tankin mai ya yi karo da wata babbar mota dauke da fasinjoji da shanu daga Wudil, jihar Kano.
Mutanen da ibtila'in ya rutsa da su sun kone har ba a iya gane su, lamarin da ya sa aka yi masu jana'izar bai daya a karamar hukumar Lapai.

Source: Twitter
An fara kokarin ceto mutane a Neja
Ahalin yanzu, jami’an FRSC da sauran hukumomin tsaro na ci gaba da kokarin ceto wadanda hatsarin tankar yau Talata ya rutsada su a jihar Neja, cewar rahoton Vanguard.
Hukumomi sun roki direbobi da su guji tuka mota cikin gaggawa ko cunkoson hanya, musamman a wannan yankin da hanyar ke cikin mummunan hali.
Tanka ta fashe cikin Zaria
A wani labarin, kun ji cewa wata tankar mai ta fashe a unguwar Dan Magaji, Zariya, jihar Kaduna, lamarin da ya jawo jama'a suka yi takansu domin tsira.
An ruwaito cewa hatsarin ya faru ne lokacin da tankar da wata motar Golf suka yi taho mu gama, kara ta tashi sannan tankar ta kama da wuta.
Shaidun gani da iso sun bayyana cewa wani hayaki mai kauri ya turnuke saman inda tankar ta ke, abin da ya sa jama’a suka rika gudu domin tsira da rayukansu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


