Tinubu Ya Nada Sabon Minista, Ya Aika Suna ga Majalisar Dattawa domin Tantancewa
- Shugaba Bola Tinubu ya mika sunan Dr. Bernard Doro ga majalisar dattawa domin tantancewa a matsayin sabon minista
- Nadin Doro ya biyo bayan nadin Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC a Yulin 2025
- Fadar shugaban kasa ta ce Dr. Doro likita ne, lauya, wanda yake da kwarewar shekaru 20 na aiki a Najeriya da Birtaniya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Dr. Bernard Doro daga jihar Filato a matsayin sabon ministan tarayyar Najeriya.
Yanzu haka dai Shugaba Bola Tinubu ya mika sunan Dr. Bernard Doro ga majalisar dattawa domin tantancewa da tabbatarwa.

Source: Twitter
Nadin minista bayan canza shugaban APC
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, wadda Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onanuga ya bayyana cewa nadin Dr. Doro ya biyo bayan nadin Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na kasa a watan Yuli.
Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa, Yilwatda yana rike da mukamin minstan ma'aikatar jin kai ne lokaci da aka nada shi shugaban APC na kasa.
Yilwatda ya zama shugaban jam'iyyar ne ba tare da wata hamayya ba a wani taro da Shugaba Tinubu da gwamnonin APC suka gudanar a Abuja.
Tinubu ya nada Doro a matsayin minista
Majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun shaida cewa Tinubu ya tattauna da mukarrabansa a daren Litinin kafin ya yanke shawarar nadin Dr. Bernard Doro.
Kuma an ce nadin Doro na daga kokarin Tinubu ya cike kujerun ministoci biyu da suka zama babu kowa kansu, ciki har da na ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, wanda ya yi murabus makonni da suka wuce.
Legit Hausa ta rahoto cewa, ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, ya yi murabus daga mukaminsa kwanaki uku bayan an fallasa shi kan amfani da takardu biyu na bogi.
Binciken jaridar Premium Times ya bankado cewa Nnaji ya gabatar da takardun kammala digiri da na NYSC na bogi ga majalisar dattawa lokacin tantance shi.

Source: Twitter
Wanene Doro, wanda Tinubu zai nada minista?
Sanarwar Bayo Onanuga ta bayyana cewa an haifi Dr. Bernard Doro a ranar 23 ga Janairu, 1969, a Kwall, karamar hukumar Bassa, jihar Filato.
Onanuga ya bayyana cewa Doro ya na da fiye da shekaru 20 na gogewa a fannoni da dama, ciki har da kiwon lafiya, magunguna, jagoranci, da ci gaban al’umma, a Birtaniya da Najeriya.
"Doro yana da digiri a fannin hada magunguna da lauyanci, da kuma MBA da ya mayar da hankali kan tsare-tsaren kasuwanci na zamani, da digirin digirgir a harkar magani.
“Yana da kwarewa a matsayin wanda ke iya ba da magani da duk wata harkar magani, wanda ke nuna irin cikakken gogewar da yake da shi a kiwon lafiya.”
- Bayo Onanuga.
Baya ga fannin aikin likita, Dr. Doro ya kasance mai kishin al’umma da jajircewa wajen ba matasa horo da shawarwari, musamman a tsakanin ’yan Najeriya mazauna kasashen waje da kuma cikin gida.
An rasa ministoci 9 a gwamnatin Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamnatin Bola Tinubu ta rasa akalla ministoci guda tara tun bayan nadinsu a watan Agustan shekarar 2023.
Daga cikinsu akwai wadanda shugaban da kansa ya sallama yayin da wasu suka yi murabus saboda wasu dalilai ko zarge-zarge.
Daga cikin ministocin da Tinubu ya tsige da kansa akwai Dr. Betta Edu, da Farfesa Tahir Mamman yayin da wadanda suka yi murabus suka hada da Uche Nnaji.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


