Magana Ta Kare: Kotun Koli Ta Shirya Raba Gardama kan Dokar Ta Bacin da Tinubu Ya Sa a Rivers
- Kotun Koli ta kusa kawo karshen shari'ar da ake yi kan dokar ta bacin da Shugaba Bola Tinubu ya sanya a jihar Rivers
- A ranar Talata, babban kotun kasar ta saurari bayanai daga bakin lauyoyin masu kara da wadanda ake kara a shari'ar
- Masu shigar da kara dai na kalubalantar matakin da Shugaba Tinubu ya dauka na dakatar da Gwamna, mataimakiyarsa da 'yan majalisa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kotun Koli taNajeriya ta shirya yanke hukunci kan karar da ke kalubalantar dokar ta bacin da Shugaba Bola Tinubu ya sa a jihar Rivers.
Karar dai wasu jihohi 11 na PDP ne suka shigar da ita, inda suke kalubalantar abin da suka kira “matakin da ya sabawa kundin tsarin mulki” da Shugaba Tinubu ya dauka a jihar Rivers.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa Kotun Kolin ta tanadi hukunci kan karar ne a ranar Talata, 21 ga watan Oktoban 2025.
Alkalan Kotun Koli za su yanke hukunci
Wani kwamitin alkalan kotun mai mutum bakwai karkashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro ya shirya yin hukuncin, bayan bangarorin da ke cikin shari’ar sun gabatar da hujjojinsu.
Masu shigar da karar su ne manyan lauyoyin gwamnati na jihohi 10, yayin da gwamnatin tarayya da majalisar dokokin ta kasa suke matsayin wadanda ake kara.
Jihohin, wadanda dukkansu ke karkashin jam’iyyar PDP, sun kalubalanci ikon shugaban kasa na dakatar da gwamna mai ci daga aiki bayan ayyana dokar ta-baci a wata jiha.
A lokacin zaman kotun, jihar Delta wacce ke matsayin mai shigar da kara ta biyar, ta janye daga cikin shari’ar, kuma lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), bai yi adawa da hakan ba, rahoton ya zo jaridar Vanguard.
Lauyoyi sun yi muhawara a kotu
Lauyan masu shigar da kara, Eyitayo Jegede (SAN), ya bayyana cewa ba wai suna kalubalantar ikon shugaban kasa na ayyana dokar ta-baci ba ne.
Sai dai, suna neman kotu ta fayyace iyakar wannan iko, musamman ko yana da ikon dakatar da gwamna, mataimakiyarsa, da 'yan majalisar dokokin jihar.
A nasa bangaren, Lateef Fagbemi (SAN), wanda ke kare gwamnati, ya ce babu wata hujja da masu kara suka bayar da ke nuna cewa an yi kuskure wajen ayyana dokar ta bacin.

Source: Twitter
Ya kuma ce ba a cire gwamna, mataimakinsa ko 'yan majalisar dokoki daga mukamansu ba, sai dai an dakatar da su na dan lokaci a matsayin wani mataki na musamman domin kawo zaman lafiya a jihar.
Daga karshe Lateef Fagbemi ya roki Kotun Koli da ta kori karar gaba dayanta.
Bayan sauraron bangarorin biyu, Kotun Koli ta bayyana cewa za ta sanar da ranar yanke hukunci daga baya.
Tinubu ya janye dokar ta baci a Rivers
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya janye dokar ta bacin da ya sanya a jihar Rivers.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: 'Yan APC sun ja kunnen shugaban jam'iyyar kan tazarcen Tinubu a 2027
Mai girma Bola Tinubu ya janye dokar ta bacin ne bayan ta cika wata shida da sanyawa sakamakon rikicin siyasa da ya addabi jihar.
Shugaban kasan ya bayyana cewa ya gamsu da ci gaban da jihar Rivers ta samu a lokacin dokar ta bacin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

