Sarkin Musulmi da Wasu Manyan Sarakunan Arewa Sun Nufi Jihar Kebbi, An Ji Dalili
- A yau Talata, 21 ga watan Oktoba, 2025, sarakunan Arewa za su gana a jihar Kebbi domin tattauna batutuwan da suka shafi yankin
- Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ne ake sa ran zai jagoranci taron a Birnin Kebbi
- Daya daga cikin manyan batutuwan da ake sa ran sarakunan za su maida hankali a kai shi ne matsalar tsaro da ta addabi Arewacin Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Sarakunan Gargajiya na Arewacin Najeriya za su gudanar da muhimmin taro kan batutuwan da suka shafi yankin yau Talata, 21 ga watan Oktoba, 2025.
Sarakunan Arewa za su yi wannan taro ne a jihar Kebbi karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmai (Sultan na Sakkwato), Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III.

Source: Facebook
Batutuwan da sarakuna za su tattauna
Jaridar Leadership ta tataro cewa taron zai tattauna matsalolin tsaro da sauran manyan al’amurra da suka addabi yankin, musamman a Arewa maso Yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa taron zai gudana ne na tsawon kwanaki biyu, daga yau zuwa gobe, a Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.
Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, ake sa ran zai bude taron, yayin da Mai Martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, shi ne mai masaukin baki.
Sarakunan da za su halarci taron Kebbi
Wani babban jami’in majalisar sarakunan Arewa ya tabbatar cewa taron zai samu halartar manyan sarakunan daga jihohin Arewa gaba ɗaya, ciki har da daga Sokoto, Kano, Katsina, Zamfara, Kaduna, Jigawa, Neja da sauransu.
Taron na zuwa ne a wani lokaci da yankin Arewa maso Yamma ke fuskantar ƙalubale na tsaro irinsu sace-sacen mutane, farmakin ’yan bindiga, da matsalar rashin zaman lafiya a kauyuka da ƙananan hukumomi.
Ana sa ran sarakunan za su tattauna hanyoyin haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da shugabannin al’umma, domin gano mafita ta gargajiya da zamantakewa wajen shawo kan matsalar tsaro da ta addabi yankin.
Haka kuma, taron zai mayar da hankali kan batutuwan ci gaban tattalin arziki, ilimi, da inganta zaman lafiya tsakanin al’ummomi daban-daban, musamman a yankunan da ake fama da rikice-rikicen makiyaya da manoma.

Source: Facebook
Sarakunan Arewa za su yi magana da murya daya
Tuni wasu daga cikin sarakuna daga sassan Arewa suka isa Birnin Kebbi tun daren jiya domin halartar wannan taron, kamar yadda Daily Post ta kawo.
Ana sa ran a ƙarshe, sarakunan za su fitar da sanarwar haɗin gwiwa kan abubuwan da suka cimma wa a tattaunawar da za su yi.
Bugu da kari, ana tsammanin sarakunan za su ba gwamnati da hukumomin tsaro hanyoyin da za su zama jagora wajen inganta tsaro, zaman lafiya da ci gaban al’umma a Arewa baki ɗaya.
Abin da ya fi damun sarakunan Arewa
A wani labarin, kun ji cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce sarakunan gargajiya sun fi damuwa da rikice-rikicen tsaro fiye da batun siyasa.
Sarkin ya bayyana haka ne a taron kwamitin zartarwan Majalisar Sarakunan Gargajiyan Arewa karo na bakwai da aka gudanar a Maiduguri, jihar Borno.
Ya jaddada cewa ba za su gaza ba wajen fadakar da shugabanni da kuma bayar da shawara don a samu zaman lafiya da kare rayukan al’umma.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


