Lokaci Ya Yi: Malamin Addinin Musulunci a Kano kuma Na'ibin Masallacin Al Furqan Ya Rasu

Lokaci Ya Yi: Malamin Addinin Musulunci a Kano kuma Na'ibin Masallacin Al Furqan Ya Rasu

  • Na'ibin Sheikh Bashir Aliyu Umar a masallacin Jumma'a na Al-Furqan Kano, Malam Aminu Adam Dorayi ya riga mu gidan gaskiya
  • Dr. Bashir Aliyu ya tabbatar da rasuwar malamin yau Talata, 21 ga watan Oktoba, 2025, ya ce za a yi jana'izarsada misalin karfe 10:00 na safe
  • Tuni dai mabiya da sauran al'ummar musulmi a Kano suka fara jaje da ta'aziyyar rasuwar Malam Aminu Adam, wanda aka bayyana da mutumin kirki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Malamin addinin musulunci a jihar Kano, Malam Aminu Adam ya riga mu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

Nnamdi kanu: 'Yan sanda sun yi bayani kan harbin masu zanga zanga a Abuja

Marigayi Malam Aminu na daya daga cikin limamanin babban masallacin Jumma'a na Al-Furqan da ke cikin birnin Kano.

Malam Aminu Adam.
Hoton na'ibin masallacin Al-Furqan Kano, Sheikh Aminu Adam. Hoto: Dr. Bashir Aliyu Umar
Source: Facebook

Fitaccen malamin addinin musuluncin kuma shugaban Majalisar Shari'a ta Najeriya, Dr. Bashir Aliyu Umar ne ya tabbatar da rasuwar Malam Aminu Adam a shafinsa na Facebook.

Dr. Bashir Aliyu Umar shi ne babban limamin masallacim Al-Furqan da ke Alue Avenue a cikin garin Kano.

Na'ibin masallacin Al-Furqan Kano ya rasu

A sanarwar da ya wallafa yau Talata, 11 ga watan Oktoba, 2025, Sheikh Bashir Aliyu ya ce Malam Aminu Adam shi ne na'ibinsa masallacin Jumma'a na Al-Furqan Kano.

Sanarwar ta ce za a yi jana'izar marigayin kamar yadda addinin musulunci ya tanada da misalin karfe 10:00 na safiya a masallacin Al-Muntadha da ke Dorayi (masallacin marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam).

Tuni dai mutane musamman jama'ar Kano suka fara tura sakon ta'aziyya da addu'ar Allah Ya jikan Malam Aminu Adam kuma ya gafarta masa kura-kuransa

An sanar da lokacin jana'izar malamin

Sanarwar ta ce:

"innalilLahi wa'inna ilaihi raji'un, Allah Ya yi wa Dan'uwa Mal. Aminu Adam Rasuwa, shi ne Na’ibin Limamin Juma’a na Masallacin Al-Furqan Kano.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta ratsa gidan sanata, ya rasa dansa da jikansa cikin sa'o'i 48

"Za a yi Jana’izarsa da Karfe 10:00 na safe (yau Talata, 21 ga watan Oktoba, 2025) a Masallacin Al-Muntada Dorayi watu Masallacin marigayi Mal. Ja’afar Mahmud Adam."

Sheikh Daurawa ya mika sakon ta'aziyya

Babban kwamandan Hisbah na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawaya yi ta'aziyyar rasuwar Malam Aminu a shafinsa na Facebook.

Sheikh Daurawa ya ce Malam Aminu ya kasance abokinsu na da'awah, mutumin kirki, ga haƙuri ga iya mu'amala, Idan yana nasiha ko khuɗuba yana yawan tunasar da mutane game da mutuwa.

"Muna addu'a Allah ya masa rahama. Allah ya yafe masa kura-kuransa. Allah ya mi shi tukwuici da aljannar Firdausi, Ya kuma bawa iyalinshi haƙurin jure wannan babban rashi da muka yi.
"Ina mika ta'aziyyata ga ɗaukacin al'ummar Musulmai, da Dr Bashir Aliyu."
Malam Aminu Adam.
Hotunan marigayi Malam Aminu Adam, na'ibin Sheikh Bashir Aliyu a masallacin Al-Furqan Kano Hoto: Dr. Bashir Aliyu Umar
Source: Facebook

Malam Kabiru Madabo ya rasu a Kano

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen malamin addinin musulunci a Kano, Malam Kabiru Ibrahim Madabo, ya kwanta dama.

Sheikh Anas Mahmud Madabo ne ya tabbatar da rasuwar malamin, yana bayyana cewa al’umma sun yi babban rashi a bangaren ilimi.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP da sakatarenta na ƙasa sun samu sabani kan takardar da aka aika wa INEC

Wannan mutuwa ta taba al'ummar Kano yayin da mutane da dama ke jimamin rasuwar tasa da kuma yi masa addu'ar samun rahama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262