Mutane 20,000 za Su Samu Ayyuka a Shirin da Kashim Shettima zai Kaddamar

Mutane 20,000 za Su Samu Ayyuka a Shirin da Kashim Shettima zai Kaddamar

  • Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, zai kaddamar da shirin NJFP 2.0 a ranar Laraba, 22 ga Oktoba, 2025 a Abuja
  • Rahoto ya ce shirin na nufin samar da aƙalla guraben ayyuka 20,000 a shekara don tallafa wa matasan da suka kammala karatu
  • An tsara shirin NJFP 2.0 ne domin samarwa matasa horo, ƙwarewa da damar kasuwanci a sassa masu muhimmanci na tattalin arziki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani shiri na musamman domin ƙara bunƙasa damar samar da ayyukan yi ga matasa ta hanyar tsarin NJFP 2.0.

Zagaye na biyu na shirin yana da nufin samar da aƙalla guraben ayyuka 20,000 a kowace shekara, tare da bai wa matasa masu karatun digiri damar koyon aiki, samun gogewa da jagoranci.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An gano masu yayata 'labarin kisan kiristoci' a Najeriya

Kashim Shettima a wani taro
Mataimakin shugaban kasa a wani taro. Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya wallafa a X cewa zai jagoranci ƙaddamar da shirin a ranar Laraba, 22 ga watan Oktoba, 2025, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Taron zai haɗa manyan jami’an gwamnati, masana’antu, da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin tattauna dabarun ƙara yawan guraben aiki da bunƙasa ƙwarewar matasa.

A yayin kaddamar da kwamitin gudanar da aikin, Shettima ya jaddada cewa NJFP 2.0 wani ɓangare ne na kokarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen samar da ayyukan yi da ƙarfafa matasa.

Shirin NJFP 2.0 da manufarsa ga matasa

Shirin NJFP, wanda aka fara a shekarar 2022, an tsara shi ne domin samar da ayyuka ga matasan Najeriya.

A matakin farko, sama da matasa 14,000 ne suka amfana ta hanyar horo na watanni 12, wanda ya taimaka musu wajen samun gogewa da damar aiki na dindindin.

Shettima ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

ASUU ta janye yajin aiki a jami'o'i, ta kafa wa gwamnatin Tinubu sharadi

“Manufar shirin ita ce canza yawan matasan da muke da su zuwa wani ƙarfi na habaka tattalin arziki ta hanyar samar musu da tsari da haɗin gwiwa.”

Ya ƙara da cewa dole ne a tabbatar da cewa shirin ya isa dukkan jihohi da yankuna na ƙasar, ba tare da la’akari da bambance-bambancen jinsi ba.

Bayanin tawagar tarayyar Turai

Jakadan Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) a Najeriya, Mista Gautier Mignot, ya bayyana cewa goyon bayan gwamnati zai taimaka wajen cimma nasarar shirin NJFP 2.0.

Wakiliyar UNDP, Elsie Attafuah, ta ce wannan shiri yana cikin babban hangen nesa na samar da tsarin da zai samar da ayyuka a faɗin ƙasa.

Mataimakin shugaban kasa, Shettima
Shettima yayin nada jagororin shirin NJFP 2.0. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Ta yaba da jajircewar Mataimakin Shugaban Ƙasa wajen jagorantar shirin, tana mai cewa abin da matasa ke buƙata shi ne ingantaccen yanayi da jarin da zai ba su damar amfani da ƙwarewarsu.

Legit ta tattauna da Adamu Ahmed

Legit Hausa ta tattauna wa wani matashi daya ce ya shirya tsaf domin cika fom din yanar gizo domin neman gurbin shiga aikin.

Adamu ya ce:

"Muna jiran damar samun aikin. Ina fata za a yi shi a bayyane domin mu samu gurbin aiki.

Kara karanta wannan

Katsina: An tsinci gawar jami'in Kwastam bayan kwana da mata 3 a otal

"Na kammala digiri shekara 2 da suka wuce, ina fatan samun aiki a wannan karon."

Tinubu ya kawo hanyar samar da ayyuka

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin kafa cibiyoyin samar da ayyuka ga 'yan Najeriya.

Karamar ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ce ta sanar da shirin yayin wani taro da ta halarta a jihar Legas.

Nkeiruka Onyejeocha ta bayyana cewa shirin na cikin matakan da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke dauka domin yaki da zaman banza.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng