Kano: 'Yar Guda Ta Fadawa Sheikh Daurawa Sharudan Auren Mai Wushirya
- Hisbah a Kano ta ce za ta shirya daura auren Basira ‘Yar Guda da Idris Mai Wushirya bayan umarnin kotu
- Shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa ya ce akwai sharuda biyar da za a bi kafin a daura auren
- Hukumar tace fina-finai ta Kano ta ce kofa a bude ta ke ga duk wanda zai taimaka wa ‘Yar Guda da Mai Wushirya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa ta fara shirin aiwatar da hukuncin kotu na daura auren fitattun masu yada bidiyo a TikTok, Basira ‘Yar Guda da Idris Mai Wushirya.
Hakan na zuwa ne bayan kotu ta bayar da umarnin a daura masu aure cikin mako takwas masu zuwa.

Kara karanta wannan
Kotu ta bada umarnin daura auren fitaccen dan TikTok da wada kan bidiyon da suka yi a Kano

Source: Facebook
A wani bidiyo da DW Hausa ta wallafa a Facebook, Sheikh Aminu Daurawa ya ce 'Yar Guda ta fadi sharadin auren Mai Wushirya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan bayyana bidiyo da suka yi a kafafen sada zumunta da ake ganin ya saba da tarbiyya da al’adun jihar Kano.
Sharudan auren 'Yar Guda da Mai Wushirya
Kwamandan hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa, ya bayyana cewa an gudanar da zaman hadin gwiwa da hukumar tace fina-finai da kuma kotu domin tsara yadda auren zai gudana.
Daurawa ya bayyana cewa akwai sharuda biyar da Hisbah ta gindaya kafin daura auren:
1. Dole ne a samu yardar juna tsakanin ma’aurata domin guje wa auren dole
2. Za a tafi asibiti a yi binciken lafiya domin tabbatar da yanayin jikinsu kafin aure
3. ‘Yar Guda ta bayyana cewa ba za ta zauna a gidan haya ba bayan aure ko kuma tare da 'yan uwan Mai Wushirya
4. Sharadi na hudu kuma shi ne biyan sadaki kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
5. Sai kuma daurin aure da yardar Allah kafin karewar wa’adin da kotu ta bayar
Ana neman iyayen ‘Yar Guda kafin aure
Sheikh Daurawa ya ce tuni an samu tattaunawa da wakilan Mai Wushirya, amma har yanzu ba a samu ganawa da iyayen ‘Yar Guda ba saboda asalinsu daga jihar Zamfara suke.
Yayin da ake nemansu, ya ce hukumar ta na ci gaba da kokarin tabbatar da cewa an bi dukkan matakan shari’a da addini kafin auren.

Source: Facebook
Duk da haka, Sheih Daurawa ya ce Hisbah ba za ta tilasta aure ba sai an tabbatar da amincewar bangarorin biyu.
Za a yi wa 'Yar Guda nasiha kafin aure
Shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano, Abba El-Mustapha, ya ce za su duba yiwuwar yin nasiha ga ‘Yar Guda kan muhimmancin amincewa da aure ko da ba shi da gidansa.
A sakon da Freedom Radio ya wallafa a Facebook, El-Mustapha ya ce kofa a bude take ga duk wanda yake son taimaka wajen ganin an gudanar da auren.

Kara karanta wannan
Dakarun soji sun fafata da ƴan bindiga, an gano ƴan China da aka yi garkuwa da su
Umarnin kotu kan 'Yar Guda da Mai Wushirya
A baya, mun rahoto cewa a ranar Litinin, kotun majistare karkashin jagorancin Halima Wali ta bayar da umarni cewa a daura auren 'Yar Guda da Mai Wushirya cikin mako takwas.
Kotun ta bayyana cewa ta dauki matakin ne don tabbatar da bin ka’idar doka bayan tuhume-tuhumen da ake musu na yada bidiyon da ake ganin ya saba doka.
Hukuncin dai ya tayar da kura, inda wasu ke ganin matakin bai dace ba, yayin da wasu kuma ke ganin hakan zai taimaka wajen gyaran tarbiyya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
