ASUU: NLC Ta Shirya, Za Ta Sa Kafar Wando Daya da Gwamnatin Tinubu
- NLC ta bayyana tsarin “babu albashi, ba aiki” domin mayar da martani ga gwamnatin tarayya a kan yajin aikin ASUU
- Ƙungiyoyin ASUU, SSANU, NASU, ASUP da sauran su za su yi haɗin gwiwa a yaƙin neman hakkokinsu daga gwamnatin
- NLC ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin makonni huɗu ta kammala tattaunawa da ƙungiyoyin ko su dauki mataki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC, tare da ƙungiyoyin ilimi da ke ƙarƙashinta, suna shirin daukar tsarin ba biyan albashi, ba aiki a matsayin martani ga gwamnatin tarayya.
Wannan na zuwa ne bayan barazanar da gwamnati ta yi wa kungiyar ASUU na hana albashi ga wadanda su ka tsunduma yajin aiki.

Kara karanta wannan
Shettima zai taso daga Abuja domin karbar wasu manyan 'yan siyasar Arewa zuwa APC

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta wallafa ce wa a NLC ta goyi bayan ASUU da kawayenta, inda ta shirya taya su ganin aikin idan aka gaza shawo kan matsalar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar NLC ta gargadi gwamnati
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa NLC ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin makonni huɗu domin ta kammala shawo kan matsalar.
A wadannan makonni, NLC na fatan gwamnati za ta tattauna sabunta yarjejeniyar shekarar 2009 da ƙungiyoyin malamai da ma’aikatan manyan makarantu.
Ƙungiyoyin da abin ya shafa sun haɗa da ASUU, SSANU, NASU, NAAT, ASUP, SSANIP, ASURI da COESU.
Kungiyoyin sun amince su yi aiki tare a matsayin ƙungiya ɗaya wajen neman hakkokinsu da kuma tsare martabarsu.
NLC ta ce:
“In ba a kammala tattaunawar cikin wa’adin ba, za mu kira taron gaggawa na ƙungiyar ƙwadago don yanke matakin yajin aiki na ƙasa baki ɗaya."
Kungiyar ta ce kusan 90% na yajin aikin da ke faruwa a Najeriya gwamnati ce ke haddasawa saboda rashin bin yarjejeniyar da ta sanya hannu kanta.
Shugaban NLC: Zaman karya yarjejeniya ya ƙare
Shugaban NLC, Kwamred Joe Ajaero, ya ce lokaci ya wuce da gwamnati ke sanya hannu kan yarjejeniya amma ta kasa cikawa, sannan ta rika barazana ga ƙungiyoyi.
Ya ce gwamnatin tarayya ce ke haddasa yajin aiki ta hanyar saba alkawuran da ta amince da su da kuma rashin bin tsari.

Source: Facebook
Ajaero ya bayyana cewa bayan tattaunawa mai zurfi da ƙungiyoyin ilimi, NLC ta yanke shawarar kafa tsarin haɗin kai don tabbatar da aiwatar da yarjejeniyoyin da aka yi a baya.
Ya ce daga yanzu, ba za su sake shiga taro da jami’an gwamnati ba idan ba su da cikakken umarni daga gwamnati.
Ajaero ya ce:
“An gama tattaunawa, an sa hannu, sai gwamnati ta koma ta ƙaryata. Wannan ba zai sake faruwa ba."
ASUU: Gwamnatin tarayya ta fusata
A baya, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fusata kwarai da gaske kan yajin aikin gargadi da ASUU ta fara na kwanaki 14 a fadin Najeriya saboda zargin watsi da bukatunta.
Ta ce, duk da kiran da aka yi wa kungiyar malaman jami'o'in na a koma teburin tattaunawa, amma ta yi kunnen ƙashi tare da tsunduma yajin aikin gargaɗin makonni biyu.
Gwamnatin tarayya ta jaddada ɗaukar matakin “ba aiki, ba albashi” ga malamai da ma’aikata da suka shiga yajin a makarantu, musamman jami’o’i da sauran manyan makarantun.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

