'Yan Bindiga Sun Sace Mutane kusan 100 a Wasu Kauyukan Zamfara
- 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutanen da ba su san hawa ba, ba su sauka ba a jihar Zamfara bayan sun kai wasu hare-hare
- Miyagun 'yan bindigan sun sace mutanen ne a wasu kauyuka guda biyu na karamar hukumar Bukkuyum bayan sun farmake su a cikin dare
- Jami'an tsaro sun fara kokarin ganin sun kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su zuwa cikin daji domin ganin an sada su da iyalinsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - 'Yan bindiga sun yi awon gaba da akalla mutane 73 yayin wasu hare-hare a jihar Zamfara
'Yan bindigan sun sace mutanen ne bayan hare-haren da suka kai kauyukan Buzugu da Rayau a cikin karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun kai hare-hare a Zamfara
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:45 na daren ranar Asabar, 18 ga watan Oktoban 2025.
'Yan bindigan waɗanda suka zo da yawa kuma ɗauke da makamai masu haɗari, sun mamaye kauyukan biyu tare da yin awon gaba da mazauna yankin zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Miyagun sun rika harbin iska don tsoratar da jama’a, kafin daga bisani su shiga gidaje suna tattara mutane cikin firgici.
Bayan sun gama da kauyen Buzugu, daga nan suka wuce Rayau, inda suka sake kama mutane da dama, ciki har da mata da yara, sannan suka nufi da su cikin daji.
An fara yunkurin ceto mutanen da aka sace
Wata majiya daga jami’an tsaro ta tabbatar da cewa an tura sojoji da ‘yan sa-kai zuwa yankin domin bin sawun masu garkuwa da mutane tare da ceto waɗanda aka sace.
"An riga an kaddamar da bincike mai zurfi domin gano inda ‘yan bindigan suka kai mutanen da suka sace. Hukumomin tsaro suna aiki tare da ‘yan sa kai na yankin domin tabbatar da cewa an dawo da zaman lafiya cikin gaggawa.”
- Wata majiya
Mummunan harin ya jefa mazauna yankin cikin tsananin tsoro da rudani, inda da dama daga cikinsu suka tsere zuwa kauyukan da ke makwabtaka da su don neman mafaka.
Jami’an tsaro sun tabbatar wa al’umma cewa suna kara kaimi wajen ayyukan tsaro, tare da haɗin gwiwa da sauran hukumomi da kungiyoyin ‘yan sa-kai, domin dawo da kwanciyar hankali a yankin.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga
- Ba sauki: Sojojin sama sun samu gagarumar nasara kan 'yan bindiga a Neja
- An shiga tashin hankali: 'Yan bindiga da makiyaya sun mamaye gari guda a Benue
- Kebbi: An ji gaskiyar zance kan batun jawo sojojin haya don yaki da 'yan bindiga
'Yan bindiga sun sace mahauta a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da wasu mahauta da dillalan dabbobi a Zamfara.
Tsagerun 'yan bindigan sun sace mutanen ne lokacin da suke kan hanyar komawa gida bayan sun halarci wata kasuwa a karamar hukumar Gusau.
'Yan uwan mutanen da aka sace sun bayyana cewa 'yan bindigan sun kira domin a kai kudin fansan daya daga cikinsu ko kuma su kashe shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


