Ministan Tinubu Ya Fasa Kwai kan Zargin Yi Wa Kiristoci Kisan Kare Dangi a Najeriya
- Ana ci gaba da muhawara kan batun yi wa Kiristoci kisan kare dangi da ake zargin ana yi a jihohin Najeriya
- Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya sake fitowa ya karyata wannan zargin da ake yadawa
- Ministan ya bayyana cewa masu yada batun kisan Kiristocin suna yi ne don lalata hadin kan da ake da shi a Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, a gwamnatin Mai girma Bola Tinubu, Mohammed Idris, ya yi magana kan batun yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.
Mohammed Idris ya bayyana cewa wadanda ke yada labarin cewa ana yin kisan kare dangi kan Kiristoci a Najeriya, suna yi ne don kokarin lalata hadin kan kasa.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce Mohammed Idris ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Abuja, yayin bude taron WPRF Abuja 2026 mai taken “Responsible Communication: The Voice of the World.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Minista ya ce kan zaluntar Kiristocin Najeriya?
Ministan ya ce dole ne Najeriya ta fuskanci barazanar bata sunanta da wasu ke yi a waje, inda ake kokarin nuna kasar tamkar wuri ne da ake zaluntar mutane bisa addininsu.
Ya musanta zargin cewa ana yi wa Kiristocin Najeriya kisan kare dangi, inda ya roki kwararrun masu hulda da jama’a da su yi amfani da iliminsu wajen kyautata kimar kasar nan a idon duniya.
"Wannan farfaganda ce da wasu daga waje suka kirkira domin raunana hadin kanmu. Sau da dama na bayyana cewa babu ko kwayar gaskiya a cikin zargin yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya."
"Don haka, ina kira gare mu da mu yi amfani da hanyoyin hulda da jama’a bisa gaskiya da hujja domin musanta irin wadannan labaran karya da ke neman bata sunan kasar mu."
- Mohammed Idris
Minista ya yabawa Shugaba Tinubu

Kara karanta wannan
'Yar ƙwaya ce fa yanzu': Sanata ya ƙaryata zargin cin zarafin matarsa a gidan aure
Mohammed Idris ya kara da cewa taron WPRF da za a gudanar a Abuja, ba kawai taron kasa da kasa ba ne, har ila yau dama ce ta nuna Najeriya a matsayin kasa mai ci gaba ta fannin sadarwa.

Source: UGC
"A karkashin shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, duniya na ganin Najeriya tana sake fasalin kanta ta hanyar kirkire-kirkire, bunkasar kasuwanci, da samun karuwar amincewa a idon duniya."
"Shirya wannan babban taro zai tabbatar da cewa Najeriya ce cibiyar sadarwa ta nahiyar Afrika kuma abokiyar hulda ta duniya wajen gina labarai na zaman lafiya, ci gaba da hadin kai."
- Mohammed Idris
Kisan Kiristoci: Majalisa ta cin ma matsaya
A wani labarin kuma, kun ji cewa wakilai ta karyata zargin da ake yi na zaluntar Kiristoci da yi musu kisan kare dangi a Najeriya.
Majalisar ta bayyana cewa babu komai a cikin zargin face karya tsantsagwaronta, domin babu gaskiya ko kadan a cikinsa.
Hakazalika, majalisar ta umurci kwamitocinta kan harkokin waje, tsaro da leken asiri, cikin gida da harkokin ‘yan sanda, da su tsara martanin diflomasiyya a hukumance.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
