Budurwa Ta Kashe Kanta Ana Shirin Yi Mata Auren Dole da Abokin Babanta
- Wata budurwa a karamar hukumar Gubio ta jihar Borno ta kashe kanta bayan mahaifinta ya tilasta mata aure da abokinsa
- Rahotanni sun bayyana cewa budurwar ta dade tana cikin damuwa saboda auren dole da aka matsa mata ta yarda da shi
- Masu kare hakkin yara sun bukaci a gudanar da bincike tare da daukar mataki domin kare ‘yan mata daga irin wannan lamari
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno – Wata budurwa a karamar hukumar Gubio ta jihar Borno ta rasa ranta bayan ta yanke shawarar kashe kanta sakamakon matsin lambar da mahaifinta ya yi mata don ta auri abokinsa.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:20 na yamma a ranar Lahadi, inda rahotanni suka bayyana cewa matashiyar ta dade tana cikin damuwa kafin ta aikata hakan.

Source: Twitter
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa lamarin ya tayar da hankali a yankin, inda jama’a ke bayyana alhini da kira ga hukumomi da su dauki mataki kan auren dole da take hakkin mata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Budurwa ta kashe kanta kan aure
Wani mai kare hakkin yara, Bukar Fantami Gubio, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai bayyana shi a matsayin abin takaici da tausayi.
A cewarsa, matashiyar ta sha bayyana rashin amincewarta da auren da aka tsara mata, tana mai cewa tana son wani daban da ta zaba da kanta.
“Damuwar da ta shiga sakamakon matsin lambar aure ne suka sanya ta ga wannan matakin. Wannan abin bakin ciki ne matuka da ke bukatar gaggawar daukar mataki,”
Inji Bukar Gubio
Kiran Gubio ga hukumomi da kungiyoyi
Bukar Fantami Gubio ya yi kira ga hukumomin kare hakkin dan Adam, jami’an tsaro da hukumomin gwamnati da su gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin, tare da tabbatar da cewa an yi adalci.
Ya ce auren dole na daga cikin manyan laifuffuka da ke tauye hakkin dan Adam, musamman na mata da ‘yan mata masu tasowa.

Kara karanta wannan
'Yar ƙwaya ce fa yanzu': Sanata ya ƙaryata zargin cin zarafin matarsa a gidan aure
“Ya kamata iyaye da shugabannin al’umma su mutunta ‘yancin ‘ya’yansu wajen zaben wanda za su aura. Wannan lamari ya zama gargadi ga duk wanda ke take ‘yancin mata,”
Inji shi
Ana jiran gwamnati ta fitar da rahoto
Har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoto, ‘yan sanda da gwamnatin jihar Borno ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Source: Facebook
Sai dai jama’a da kungiyoyin kare hakkin yara kamar Bukar Gubio suna bukatar gwamnati ta kafa dokoki masu tsauri don hana auren dole da kare mutuncin ‘yan mata a jihar da kasa baki daya.
An kama amarya da ango a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama wasu mutane da ake zargin sun daura aure ba bisa ka'idar addini ba.
Bayanan da hukumar ta fitar sun tabbatar da cewa an kama amarya, ango da wadanda suka shaida daurin auren.
Hisbah ta kama su ne bisa zargin daura aure ba tare da izinin iyaye ba, kuma an daura auren ne a bisa sadaki N10,000.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
