'Paul Biya Ya Fadi,' Dan Adawar Kamaru da Ya Yi Ikirarin Cin Zabe zai Fitar da Sakamako
- Rahotanni sun fara fitowa game da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Kamaru a makon jiya
- Dan adawa, Issa Tchiroma Bakary ya ce zai fitar da rahoton asali na rumfunan zabe domin tabbatar da nasararsa
- Issa Tchiroma ya yi watsi da sakamakon wucin gadi da ke nuna shugaban kasar mai ci, Paul Biya, na kan gaba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kamaru – Dan jam'iyyar adawa a zaben shugaban kasa na Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya bayyana cewa zai wallafa rahoton asali na rumfunan zabe.
Issa Tchiroma Bakary ya ce zai fitar da sakamakon ne domin tabbatar da cewa shi ne ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 12 ga Oktoba, 2025.

Source: Getty Images
Daily Trust ta rahoto cewa hakan na zuwa ne a daidai lokacin da sakamakon farko daga hukumar zabe ke nuna cewa shugaban kasar mai ci, Paul Biya, yana kan gaba.
Tchiroma ya ce matakin nasa na nufin tabbatar da gaskiya da kaucewa duk wani yunkuri na karkatar da sakamakon zaben.
An kalubalanci sakamakon zaben kasar Kamaru
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Tchiroma ya bayyana cewa tawagar kamfen dinsa na shirin fitar da sahihan bayanai daga rumfunan zabe da aka sanya hannu a kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa sakamakon da zai fitar jami’an sa ne suka tattara:
“Domin tabbatar da gaskiya da kuma hana duk wani magudi, tawagar mu za ta wallafa sahihan rahotannin rumfunan zabe da aka tattara daga jami’an mu da suka kasance a wuraren kada kuri’a.”
Dan takarar, wanda ke jagorantar jam’iyyar FSNC, yana da goyon bayan kawancen jam’iyyun adawa da ake kira Union for Change.
Ya ce wannan mataki na nufin kare kuri’un ‘yan kasa da tabbatar da cewa ra’ayin jama’a bai sauya ba a hannun masu mulki.
Paul Biya na kan gaba bisa rahoton farko
Shugaban kasar Kamaru, Paul Biya, wanda ya j ke agoranci kasar tun daga shekarar 1982, na neman karin wa’adin mulki duk da kiraye-kirayen da ake yi masa da ya sauka daga karaga.
Sakamakon wucin gadi daga hukumar zabe ya nuna Biya na samun rinjaye a wasu manyan birane, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga bangaren adawa.
Wasu yankuna na kasar sun fara gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da irin wannan sakamakon da ke fitowa daga hukumar.
Ana zargin an karkatar da zaben Kamaru
Tchiroma ya yi zargin cewa hukumar zabe da wasu jami’an gwamnati na shirin amfani da karfin iko wajen canza sakamakon.
Legit ta rahoto ya ce ya zama dole a tabbatar da gaskiya domin kada ‘yan kasa su rasa amincewa da tsarin zabe baki daya.

Source: Getty Images
Wani jigo a jam’iyyar FSNC ya ce za su bi doka da ka’ida wajen kare kuri’un su amma ba za su lamunci magudi ba.
Zabe: An yi zanga zanga a Kamaru
A wani rahoton, kun ji cewa an fara zanga-zanga, musamman a yankunan da ke da goyon bayan jam’iyyun adawa a kasar Kamaru.
‘Yan sanda sun karfafa tsaro a babban birnin kasar, Yaoundé, domin hana barkewar tarzoma yayin da kirga kuri’u ke cigaba.
Hakan na zuwa ne yayin da hukumar zabe ke ci gaba da tantance sakamakon daga rumfuna daban-daban kafin fitar da hukuncin karshe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

