Sauƙi Ya Samu: Ƴan Kasuwa Sun Rage N700 daga Farashin Gas ɗin Girki a Najeriya
- Farashin kilo na gas ɗin girki ya sauka daga N2,000 zuwa tsakanin N1,300 da N1,500 bayan karuwar wadatar kayayyaki
- Shugaban masu sayar da gas, Ayobami Olarinoye, ya ce farashin zai iya raguwa idan gas din ya ci gaba da wadata
- Yayin da 'yan Najeriya ke fatan farashin ya koma kasa da N900, ita kuma gwamnati ta sa ido kan dillan da ke boye gas din
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - 'Yan kasuwa sun bayyana cewa farashin gas ɗin girki (LPG) ya sauka daga N2,000 kan kowane lita zuwa tsakanin N1,300 da N1,500 a karshen makon nan.
Shugaban ƙungiyar masu sayar da gas din girki a Najeriya (LPGAR), Ayobami Olarinoye, ya tabbatar da wannan ci gaban a ranar Lahadi.

Source: UGC
Farashin gas din girki ya fara sauka
A zantawarsa da jaridar Punch, Ayobami ya ce an samu karuwar isar da kayayyaki, lamarin da ya taimaka wajen rage farashin, kodayake farashin bai kai ga daidaita a ko ina ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“An fara samun wadatuwar gas din a kasuwa. Yanzu ana samun karin gas din daga masana’antu.
"Wannan ya sa farashin ya fara sauka, amma bai dawo da yadda yake da ba. Yanzu ana sayar da 1kg tsakanin N1,300 da N1,600, ya danganta da yankin da ake sayarwa."
- Ayobami Olarinoye.
Olarinoye ya kara da cewa yana sa ran kasuwar za ta daidaita cikin mako guda idan 'yan kasuwa sun ci gaba da samun isasshen gas din.
Ya kara da cewa:
“Kasuwar bata daidaita ba tukuna, amma akwai ci gaba. Idan aka ci gaba da samun wadatuwa gas, farashi zai ragu fiye da haka nan gaba kadan."
Ana fatan farashin gas ya kara sauka
Wasu masu amfani da gas sun bayyana farin ciki da wannan saukar farashi, amma suna fatan farashin 1kg ya dawo kasa da N900 kamar yadda yake kafin ya tashi.
Idan za a tuna, farashin 1kg na gas din girki ya tashi daga N1,000 zuwa kusan N2,000 a watan da ya gabata, bayan yajin aikin kungiyar PENGASSAN da rikicin ta da matatar man Dangote.
Ko bayan da aka dakatar da yajin aikin, farashin bai sauka nan da nan ba, abin da ya kara tsadar rayuwa ga ‘yan Najeriya.

Source: UGC
Gwamnati ta gargadi dillalan gas din girki
Ministan mai na ƙasa mai kula da sashen iskar gas, Ekperikpe Ekpo, ya shiga cikin lamarin a makon da ya wuce, inda ya yi barazanar hukunta masu boye kaya ko masu tauye abokan hulda.
Domin tabbatar da hakan, ministan ya umarci hukumar NMDPRA ta tsaurara sa ido kan dillalan gas don dakile boye kaya da ko wani abu da zai jawo karuwar kudin, inji rahoton Business Day.
A cewar Olarinoye, akwai bambanci tsakanin farashin da matatar Dangote ke sayar da gas da kuma farashin da manyan dillalai ke sayar da shi.
“Dangote na sayar da LPG a N15.8 miliyan ga manyan dillalai, amma suna sake sayarwa ga ‘yan kasuwa a tsakanin N18.4m da N18.5m."
- Ayobami Olarinoye.
Wannan mataki, a cewar masana, ya nuna cewa akwai bukatar gwamnati ta sa ido sosai domin ganin farashin gas ya ci gaba da sauka har zuwa yadda yake a baya.

Kara karanta wannan
APC za ta ci gaba da raunata 'yan adawa, Yilwatda ya fadi manyan ADC da za su koma jam'iyyar
Dangote ya rage kudin gas din girki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Alhaji Aliko Dangote ya tabbatar da rage farashin gas din girki (LPG) a matatarsa domin saukaka wa ’yan Najeriya.
Matakin zai taimaka wajen daidaita farashin gas din girki a kasuwar cikin gida, musamman a lokacin da ake fuskantar karancin gas a wasu yankuna.
Kamfanin mai na NNPCL ya yaba da wannan mataki na Dangote, yana kiran shi da ci gaba mai kyau ga tattalin arzikin kasa da saukaka wa 'yan Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

