Asiri Ya Tonu, an Kama Hatsabiban Yan Bindiga da Suka Hallaka Sarki Mai Martaba
- Jami’an tsaro sun cafke wasu manyan hatsabiban ‘yan ta’adda biyu tare da masu daukar nauyinsu, inda aka kwato bindigogi, harsasai
- Daya daga cikin wadanda aka kama, Paschal Ibuaku, ya amsa laifin shiga ta’addanci, garkuwa da mutane, fashi da kuma kisa
- An kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi da daukar nauyin kungiyar, Magnus Ejiogu da Miletus Ihueze
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Owerri, Imo - Jami’an tsaro sun samu galaba kan miyagun yan bindiga inda suka samu manyan makamai wanda suke amfani da su domin kai hare-hare.
Jami'an a jihar Imo sun yi nasarar cafke manyan hatsabiban ‘yan ta’adda biyu tare da masu daukar nauyinsu bayan wani samame da suka kai a wasu kananan hukumomi.

Source: Facebook
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da haka a shafin X inda ya ce an kwato bindigogi, harsasai da kayan tsafi daga hannunsu.

Kara karanta wannan
Ta tabbata, sojojin Najeriya sun kama hatsabibin ɗan ta'adda da aka jima ana nema
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda yan bindiga ke kai hare-hare a Imo
Jihar Imo na daga cikin jihohin Kudu maso Gabas a Najeriya da suke shan fama da matsalolin tsaro.
A baya, gwamnatin jihar Imo ta yi alkawarin yin duk abin da ya dace don ganin ta ceto Ngozi Ogbu, tsohon ɗan majisa da aka sace.
A ranar 7 ga Satumba, 2025 ne wasu da ake zargin 'yan kungiyar IPOB ne, ɗauke da makamai suka sace Mista Ngozi.
Wadanda suka sace tsohon dan majalisar, sun ce za su kashe shi idan gwamnati ba ta biya bukatunsu a kwanaki hudu ba.

Source: Original
Wadanda aka kama kan zargin ta'addanci a Imo
Majiyoyi sun nuna cewa an kama daya daga cikin su, Paschal Ibuaku, a Obudi Agwa yayin da yake daukar sababbin ‘yan kungiyar IPOB/ESN.
Ya amsa laifin shiga ta’addanci, fashi, garkuwa da mutane da kisan kai, ciki har da kashe Sarkin Agwa, Eze Dr. I.O. Asor, a ranar 14 ga Oktoba, 2022.
Haka kuma, an cafke wasu mutane biyu da ake zargin sun dauki nauyin ta’addancin, Magnus Ejiogu da wani boka mai suna Miletus Ihueze.
Matakan da jami'an tsaro suka dauka kan lamarin
Ejiogu ya biya Naira miliyan daya domin kashe Sarkin, yayin da Ihueze ya bayar da miliyan hudu da taimakon tsafi saboda rikicin fili.
Jami’an tsaro sun ce ana cigaba da bincike kan wadanda aka kaman, kuma wadanda suka tsere za a kamo su.
Yan bindia sun yi barna a Katsina
Mun ba ku labarin cewa ‘yan bindiga a Katsina sun kai wani hari a jihar ta wani irin sabon salo wanda ya jawo asarar dukiyoyi bayan kakaba haraji kan manoma da suke shirin girbe amfanin gona.
An tabbatar da cewa maharan tara shanun sata sama da 200, suka sako su cikin gonaki a karamar hukumar Kankia da ke jihar da ke Arewacin Najeriya.
Sun kuma bukaci mazauna Kada su biya kuɗin fansa ₦4m, tare da barazanar hana su girbi idan ba su biya ba wanda hakan ya yi matukar tayar da hankulan mazauna yankin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
