Ba Sauki: Sojojin Sama Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Bindiga a Neja

Ba Sauki: Sojojin Sama Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Bindiga a Neja

  • Dakarun sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta kan 'yan bindiga a jihsr Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga da dama bayan sun yi musu luguden wuta a cikin daji
  • Nasarar da sojojin suka samu ta karfafa gwiwar mutanen yankin wadanda suka dade suna fama da hare-haren 'yan bindiga

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) ta kai mummunan hari ta sama kan tawagar ’yan bindiga da ke ta’addanci a jihar Neja.

Rundunar sojojin saman ta hallaka 'yan bindiga da dama wadanda suka addabi kauyukan karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.

Sojojin sama sun hallaka 'yan bindiga a Neja
Jiragen saman dakarun sojojin sama na Najeriya Hoto: Sodiq Adelakun
Source: Getty Images

Jaridar The Guardian ta ce shaidun gani da ido sun bayyana cewa an kai harin ne kan 'yan bindigan da ke hanyar tafiya bayan sato shanu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan bindiga

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun watsa daruruwan shanun sata 200 cikin gonaki, sun bukaci haraji

'Yan bindigan suna wucewa ne ta garuruwan Yabawa, Bazana, Awallah, Dankolo, da Kumbashi, zuwa Kakihum.

An bayyana cewa jiragen yakin na NAF sun kai harin ne daidai lokacin da ’yan bindigan ke tafiya dauke da shanun sata daga Ragada da wasu kauyuka.

Jiragen yakin sun yi ruwan bama-bamai wanda hakan ya jawo aka hallaka da dama daga cikinsu, sauran kuma suka gudu.

"Lokacin da jirgin ya fara harbi, Allah ne ya cece ni, domin ina hannunsu kafin harin."

- Wani da ya tsira

Shaidu daga nesa sun bayyana cewa sun ji fashe-fashe da dama tare da ganin hayaki mai yawa yana tashi daga wurin, yayin da ’yan bindigan suka rarrabu cikin firgici.

Sojojin kasa da ke Rijau, Warari da Gulbin Boka sun ba da hadin kai ta hanyar toshe hanyoyin tserewa da kuma kare al’ummomi daga yiwuwar ramuwar gayya.

Mazauna yankin sun yaba wa wannan aikin, suna kiran shi a matsayin hari mafi nasara da dakarun Najeriya suka kai a wannan yanki cikin ’yan shekarun nan.

Kara karanta wannan

Dakarun soji sun fafata da ƴan bindiga, an gano ƴan China da aka yi garkuwa da su

Wannan nasarar harin ta kara karfafa gwiwar jama’a da aminci ga rundunar sojojin Najeriya, tare da tabbatar da kudirin gwamnati na kawo karshen ta’addanci a yankin Neja da Najeriya gaba ɗaya.

Sojojin sama sun kashe 'yan bindiga a Neja
Taswirar jihar Neja, tarayyar Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan sojoji

Sojoji sun jefa bama-bamai kan 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sama na rundunar Operation Hadin Kai sun kai hare-hare masu zafi kan 'yan ta'adda a jihar Borno.

Farmakin da sojojin saman suka kai sun yi sanadiyyar hallaka da dama daga cikin ‘yan ta’addan tare da rusa gine-ginen su a jihar Borno.

Dakarun sojojin dai sun kai harin ne bayan samun bayanan sirri kan motsin ‘yan ta’adda a Bula Madibale cikin yankin Gezuwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng