Yan Bindiga Sun Watsa Daruruwan Shanun Sata 200 cikin Gonaki, Sun Bukaci Haraji

Yan Bindiga Sun Watsa Daruruwan Shanun Sata 200 cikin Gonaki, Sun Bukaci Haraji

  • ‘Yan bindiga a Katsina sun kai wani hari a jihar ta wani irin sabon salo wanda ya jawo asarar dukiyoyi bayan kakaba haraji
  • An tabbatar da cewa maharan tara shanun sata sama da 200, suka sako su cikin gonaki a karamar hukumar Kankia da ke jihar
  • Sun kuma bukaci mazauna Kada su biya kuɗin fansa ₦4m, tare da barazanar hana su girbi idan ba su biya ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kankia, Katsina - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa wasu yan bindiga dauke da makamai sun kuma kai farmaki a jihar Katsina.

Majiyoyi daga Jihar Katsina sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun tara shanun sata fiye da 200, sannan suka sako su cikin gonaki.

Yan bindiga sun sanya haraji ga yan kauye a Katsina
Gwamna Dikko Umaru Radda yayin taro kan tsaro a Katsina. Hoto: Dikko Umaru Radda.
Source: Facebook

Rahoton shafin Bakatsina da ke fashin baki kan lamuran tsaro ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a yankin karamar hukumar Kankia.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya barke a wani yankin Kaduna, an kashe fiye da mutane 5 a rana 1

Yadda ake ci gaba da sulhu da yan bindiga

Dukkan wannan hare-hare na zuwa yayin wasu yankunan a jihar Katsina ke ci gaba sulhu da yan bindiga domin zaman lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kananan hukumomi uku a Katsina sun shiga yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindiga domin dakatar da hare-hare a yankin.

Shugaban karamar hukumar Bakori ya ce tattaunawa da fahimtar juna ne ginshiƙin samun zaman lafiya mai dorewa a Katsina.

Wasu mutane dai sun nuna shakku kan sabuwar yarjejeniyar bayan irinta da aka yi a wasu garuruwa ta gaza haifar da ɗa mai ido.

Yadda yan bindiga ke sheke ayarsu a jihar Katsina
Taswirar jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yan bindiga sun tura shanu cikin gonaki

Majiyoyi suka ce lamarin da ya jawo lalacewar amfanin gona da dama da kuma asarar miliyoyin Naira ga mazauna yankin.

Baya ga haka, maharan sun kai farmaki ƙauyen Huntumai inda suka shiga gidajen mutane suka fasa suka sace kayayyaki da dukiyoyin jama’a.

Rahotanni sun kara cewa ‘yan bindigar sun nemi kuɗin fansa na ₦4 miliyan daga mazauna Kada, tare da gargadin cewa za su hana su yin girbi idan ba su biya kudin ba.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun lallaba cikin masallaci ana sallar asuba, sun sace mutane

Sanarwar ta ce:

"Rahotanni daga Jihar Katsina sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun tara shanun sata fiye da 200, suka sako su cikin gonaki a Karamar Hukumar Kankia, inda suka lalata amfanin gona.
"Haka kuma, sun kai hari ƙauyen Huntumai inda suka fasa gidaje suka sace kayayyaki.
"Ana kuma rahoton cewa maharan sun bukaci mazauna ƙauyen Kada su biya kuɗin fansa na Naira miliyan huɗu (₦4m), tare da barazanar hana su yin girbi idan ba su biya kudin ba."

Gwamna ya magantu kan sulhu da yan bindiga

A baya, mun baku labarin cewa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya tabo batun yin sulhu da 'yan bindiga a gwamnatinsa.

Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taba shiga tattaunawa da 'yan bindiga ba saboda wasu dalilai inda ya yi karin haske kan sulhu da wasu ke yi.

Gwamnan ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta bude kofar goyon bayan yarjejeniyar zaman lafiya da al'umma suka shirya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.