Dakarun Soji Sun Fafata da Ƴan bindiga, an Gano Ƴan China da Aka Yi Garkuwa da Su

Dakarun Soji Sun Fafata da Ƴan bindiga, an Gano Ƴan China da Aka Yi Garkuwa da Su

  • Rundunar sojin Najeriya ta ceto mutane 21 da aka sace a kwanan nan, ciki har da wasu ‘yan kasar China guda hudu
  • An kaddamar da farmakin ne a karkashin Operation FANSAN YAMA domin murkushe ‘yan bindiga a Arewa ta Tsakiya
  • Rundunar sojin ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan bindiga, tare da hadin gwiwa da NAF da sauran hukumomi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara – Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa dakarunta sun samu nasarar ceto mutane 21 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Daga cikin mutane 21 da aka ceto, akwai ‘yan kasar China hudu, kuma an kubutar da su ne a wani aikin hadin gwiwa da aka gudanar a jihohin Kwara da Kogi.

Sojojin Najeriya sun kubutar da mutane 21, ciki har da 'yan China da aka yi garkuwa da su
Wani sojan Operation FANSAN YAMMA ya dauko daya daga cikin wadanda aka kubutar da su daga 'yan bindiga. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun ceto mutane 21 daga 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Matasa sun taso Shugaba Tinubu a gaba, suna so a tsige mamba a hukumar NDDC

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na sojoji, Laftanar Kanal Polycarp Okoye, ya fitar a ranar Asabar, a shafin rundunar na X.

Laftanar Kanal Polycarp ya bayyana cewa sojoji sun kai samamen ne ne a ranar Juma’a, 17 ga Oktoba, 2025, karkashin Operation FANSAN YAMA.

Ya ce aikin ya kasance wani yunkuri na ci gaba da murkushe ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ke addabar yankin Arewa ta Tsakiya, musamman a cikin dazukan da ke kan iyakar Kwara da Kogi.

“Dakarun rundunar 2 Division tare da Sector 3 sun gudanar da farmaki inda suka ceto mutane 21 da aka sace daga wurare daban-daban a cikin jihohin biyu."

- Laftanar Kanal Polycarp Okoye.

‘Yan China da 'yan Najeriya sun sha wahala

Wata sanarwa ta tabbatar da cewa mutanen da aka ceto sun hada da maza 14, mata 5, jariri daya da kuma ‘yan China hudu.

Wasu daga cikin wadanda aka ceto, in ji Okoye, sun kasance a hannun masu garkuwa da su fiye da watanni hudu, kafin sojojin su kai farmaki mai karfi wanda ya tilasta wa ‘yan bindigar barin fursunonin su.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu, an kama hatsabiban yan bindiga da suka hallaka Sarki Mai Martaba

“Bayan samun rahotanni daga cikin dazuka, dakarunmu sun kara tsananta farmaki wanda ya sanya ‘yan bindiga suka tsere, suka bar wadanda suka sace,” in ji Okoye.

Bayan an kubutar da su, an garzaya da dukkan wadanda aka ceto zuwa asibitin rundunar soji domin samun kulawar gaggawa da cikakken binciken lafiya.

Sojoji sun fafata da 'yan bindiga, sun ceto mutane 21 da aka sace a Kwara da Kogi
Wasu daga cikin mutanen da sojoji suka ceto daga hannun 'yan bindiga a Kwara da Kogi. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun gode wa hukumomin tsaro

Okoye ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan ta ba tare da sassauci ba domin tabbatar da cewa babu wurin buya ga masu aikata laifi a yankin.

“Ba za mu ba wa ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane damar samun mafaka ba,” in ji shi.

Babban kwamandan rundunar 2 Division ya gode wa Rundunar Sojin Sama (NAF) saboda goyon bayan da ta ba su ta sama, tare da yabawa hadin gwiwar da aka samu daga sauran hukumomin tsaro.

An kama masu hada baki da 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dubun wasu masu hada baki da 'yan ta'adda ta cika bayan sun fada komar jami'an tsaro a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Ana jita jitar juyin mulki, an gargadi masu zanga zanga kusantar fadar Tinubu

Dakarun sojoji tare da hadin gwiwar jami'an rundunar C-Watch sun samu nasarar cafke mutanen da ake zargi bayan gudanar da bincike.

Hakazalika, sojojin sun kuma samu nasarar ceto wani mutum da 'yan ta'adda suka dauke yana tsaka da aiki a gonarsa kuma suka azabtar da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com