Bankin Duniya Ya Fadi Bala’in da Zai Faru a Najeriya kan Karuwar Yawan Al’umma
- Shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga, ya yi hasashen yawan al'ummar Najeriya zai karu nan da wasu sheakru
- Bankin ya ce rashin shirin bai daya na iya jefa matasa cikin tashin hankali da rashin kwanciyar hankali.
- Ya ce yawan jama’ar Najeriya na iya ƙaruwa da mutum miliyan 130 nan da 2050, abin da zai iya zama barazana
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga, ya yi fargaba kan yawan karuwar al'umma a Najeriya nan da wasu shekaru.
Bankin ya gargadi cewa idan ba a samu hadin kai na duniya ba, karuwar yawan matasa na iya zama barazana ga zaman lafiya.

Source: UGC
Barazanar da ke tunkarar Najeriya
Punch ta ce Banga ya bayyana haka ne yayin taron shekara na Bankin Duniya da IMF na 2025, inda ya ce yawan jama’ar Najeriya na iya ƙaruwa da miliyan 130 kafin 2050.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Banga ya ce karuwar jama’a a Afirka tana iya kawo barazana, yana mai cewa rashin ayyukan yi na iya haifar da tarzoma da hijira.
Ya bayyana cewa idan aka zuba jari cikin matasa ta hanyar samar da dama, za su iya zama ginshikin ci gaba da kirkire-kirkire a nan gaba.
Banga ya ce nan da 2050 sama da kashi 85 cikin 100 na mutane za su rayu a kasashen da ake kira masu tasowa.
Ya kara da cewa nan da shekaru 10 zuwa 15, matasa biliyan daya da dubu dari biyu za su fada neman aiki amma akwai guraben aiki miliyan 400 kacal.
Yadda al'umma za su karu a Afirka
A cewarsa, hakan yana nufin matasa miliyan 800 za su zama marasa aiki ko kuma masu aiki mara tsari a fadin duniya, kamar yadda BusinessDay ta ruwaito.
Ya yi nuni da cewa Afirka ce ke kan gaba wajen karuwar jama’a, inda Najeriya za ta kara da mutane miliyan 130 kafin shekara ta 2050.
Banga ya ce matasa da hazakarsu za su iya sauya yanayin duniya idan aka mayar da hankali wajen samar da dama maimakon tallafin bukata kawai.
Ya gargadi cewa idan ba a dauki mataki ba, fatan matasa zai iya koma wa cikin takaici, ya haddasa tashin hankali da rashin tsaro.

Source: Getty Images
Alakar yawan jama'a da tattalin arziki
A cewar Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai lura da yawan jama’a, Najeriya yanzu tana da mutane miliyan 237.5, ita ce mafi yawan jama’a a Afirka.
Tare da karin mutane miliyan 130 da ake tsammani, Najeriya na iya zama cikin manyan kasashen duniya masu yawan matasa da jama’a.
Banga ya bayyana Afirka a matsayin cibiyar wannan sauyi na yawan jama’a, inda ya ce tattalin arziki ba ya bin saurin haihuwa.
Bankin Duniya ya yabawa salon mulkin Tinubu
Kun ji cewa Bankin Duniya ya ce Najeriya ta samu nasara bayan cire tallafin man fetur da hada tsarin kudin kasashen waje da wasu bangarori.
Bankin ya bukaci gwamnatin tarayya ta kara haraji a wasu bangarori da kuma rage kashe kudin da bai da amfani.

Kara karanta wannan
'An fi kashe Musulmi,' Hadimin Trump ya karyata zargin kisan Kiristoci a Najeriya
Ya kuma shawarci gwamnati da ta binciki NNPC, ta sabunta dokokin saye da kasafin kudi, tare da barin Naira ta daidaita da kasuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

