'Babbar Matsalar da Najeriya Ke Fuskanta Yanzu,' Atiku Ya ba Tinubu Shawarwari

'Babbar Matsalar da Najeriya Ke Fuskanta Yanzu,' Atiku Ya ba Tinubu Shawarwari

  • Atiku Abubakar ya ce babban kalubale da Najeriya ke fuskanta shi ne talauci, wanda ke jawo rashin tsaro da sauran matsaloli
  • Ya bukaci gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kungiyoyi da al’umma da su hada kai wajen yaki da talauci tun daga tushe
  • Maganar Atiku na zuwa ne bayan Bankin Duniya ya ce 'yan Najeriya miliyan 139 na rayuwa cikin talauci saboda hauhawar farashi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya yi magana game da karuwar talauci a Najeriya.

Atiku, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya bayyana damuwarsa kan yadda talauci ke kara kamari a Najeriya duk da albarkatun da kasar ke da su.

Atiku Abubakar ya ce babban kalubalen da Najeriya ke fuskanta shi ne talauci.
Alhaji Atiku Abubakar yana daga wa magoya bayan PDP baya a gangamin zaben 2023. Hoto: @atiku
Source: Twitter

'Talauci ya yi katutu a Najeriya,' Atiku

Fitaccen dan siyasar ya bayyana ra'ayinsa a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar domin tunawa da Ranar Yaki da Talauci ta Duniya.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin APC ta jawo yunwa da matsalar tsaro a Najeriya, ADC ta fasa kwai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Atiku ya ce Najeriya na cikin kasashen da talauci ya fi yi wa katutu, duk da arzikin da take da shi na ma’adinai, noma da albarkatun dan Adam.

Ya ce talauci yana haifar da matsaloli masu yaduwa kamar rashin lafiya, jahilci, tsaro da bege.

Atiku ya bayyana cewa talauci shi ne babban abokin gabar dan Adam, domin yana lalata rayuwa da cigaban al’umma gaba daya.

“Inda talauci ya kafa tushe, sai ka ga jahilci, cututtuka, rashin tsaro da rashin kyakkyawan tunani suna biyo baya,” in ji Atiku.

Atiku ya aika sako ga gwamnatin Tinubu

Atiku ya bayyana Ranar Yaki da Talauci a matsayin kira ga kasashe su dauki mataki. Ya bukaci gwamnatin Bola Tinubu da gwamnonin jihohi da kungiyoyin fararen hula su dauki tsare-tsaren tallafi masu dorewa don taimaka wa talakawa.

Ya ce dole ne a dauki yaki da talauci zuwa kowane gida, gari da makaranta, domin kowane dan Najeriya ya zama bangare na mafita.

Kara karanta wannan

'An fi kashe Musulmi,' Hadimin Trump ya karyata zargin kisan Kiristoci a Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa rashin cin abinci da talauci suna barazana ga zaman lafiya da tsaro a kasar nan.

“Idan talaka ya ji yunwa, zaman lafiya na kwana a waje,” in ji shi, yana mai jaddada cewa yaki da talauci hanya ce ta dawo da mutunci da zaman lafiya.

Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin tarayya ta hada kai da kungiyoyi domin samar da sauki ga talakawa
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Atiku Abubakar a wani taro suna raha. Hoto: @atiku
Source: Twitter

'Yan Najeriya miliyan 139 na rayuwa a talauci

Sanarwar Atiku ta biyo bayan rahoton Bankin Duniya wanda ya nuna cewa mutane miliyan 139 na rayuwa cikin talauci a Najeriya.

Legit Hausa ta rahoto cewa Bankin Duniya ya ce hauhawar farashin abinci, rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki na kara jefa mutane cikin halin kunci.

Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ya bayyana hakan a wani taron da aka gudanar a Abuja, inda ya ce sauye-sauyen tattalin arziki ba su isa ga talaka ba.

'Talauci ya yi muni a Najeriya' - El-Rufai

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ce 'yan Najeriya suna ci gaba da fada wa cikin kangin talauci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta jero abubuwan da suka jawo karyewar farashin abinci warwas

Amma a ganinsa, akwai sakaci a dalilin da ya sa lamarin ke ta'azzara, inda ya buga misali da kasahen da ke ci gaba a yanzu.

A hannu guda kuma, Malam Nasir El-Rufa'i ya koka a kan yadda aka samu raguwar yawan masu kada kuri’a zuwa 30%, kamar yadda aka gani a 2023.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com