APC Ta Yi Martani bayan Bullo da Wani Shirin Kifar da Tinubu a 2027
- Jam'iyyar APC mai adawa a Najeriya ta tanka bayan an bukaci 'yan adawa su yi amfani da siyasar kabilanci don kifar da Shugaba Bola Tinubu a babban zaben 2027
- Mai magana da yawun jam'iyyar APC a jihar Legas, Mista Seye Oladejo, ya bayyana cewa 'yan Najeriya sun riga sun waye wajen sanin abin da ke yi musu ciwo
- Seye Oladejo ya bayyana cewa 'yan adawa sun yi kadan su kifar da Shugaba Tinubu a zaben 2027, saboda ayyukan da yake yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta yi magana kan tazarcen shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa siyasar kabilanci ba za ta iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu sake lashe zabe a shekarar 2027 ba.

Kara karanta wannan
APC za ta ci gaba da raunata 'yan adawa, Yilwatda ya fadi manyan ADC da za su koma jam'iyyar

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce mai magana da yawun jam’iyyar APC a jihar, Mista Seye Oladejo, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Legas ranar Asabar, 18 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kifar da Tinubu: Jam'iyyar APC ta yi martani
Mista Seye Oladejo ya mayar da martani ne ga Cif Dele Momodu, tsohon jigo a PDP wanda yanzu ya koma ADC, bayan ya shawarci jam’iyyun adawa su haɗu su yi amfani da kabilanci domin kayar da Tinubu a 2027.
Mai magana da yawun na APC ya yaba wa Momodu saboda ya farka daga bacci wajen gane cewa ba za a iya dakatar da Shugaba Tinubu ba a siyasance, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar da labarin.
“Ya kamata a sani cewa zamanin amfani da kabilanci a matsayin hanya ta mallakar mulki ya wuce."
’Yan Najeriya sun waye. Yanzu suna kallon wanda zai iya yin aiki, ba wanda zai raba kasa ba.”
- Mista Seye Oladejo
APC ta cika baki kan Tinubu
Ya kara da cewa karkashin jagorancin Tinubu, Najeriya tana sake gina kanta a bisa ginshikai na adalci, haɗin kai da sauye-sauyen tattalin arziki.

Source: Facebook
Oladejo ya kuma shawarci Momodu da ya fara sanin waye shi a siyasance, kafin ya fara ba wasu shawara.
“A gaskiya, masu hangen nesa a siyasa sun riga sun amince cewa jam’iyyun adawa ba za su iya kayar da APC a 2027 ba – ko da suna hade, ko da suna rarrabe."
"Zaben 2027 zai kasance gwajin cancanta da aiki, ba na kabilanci ko tarihin baya ba. Kuma irin siyasar da Dele Momodu ke yi, ba za ta samu gurbi a wannan lokaci ba."
- Mista Seye Oladejo
Wike ya yi maganar takara da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya yi martani kan rahotannin da ke cewa yana shirin yin takara da Shugaba Bola Tinubu a zaben shekarar 2027.
Wike ya bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a cikin jita-jitar, ya zargi masu yadata da kokarin bata masa suna.
Ministan ya bada tabbacin cewa zai ci gaba da goyon bayan Shugaba Bola Tinubu har zuwa shekarar 2031.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

