Zaben 2019: Yadda Akpabio Ya Yi Karyar an Yi Masa Magudin Zabe a gaban Sanatoci

Zaben 2019: Yadda Akpabio Ya Yi Karyar an Yi Masa Magudin Zabe a gaban Sanatoci

  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi ikirarin cewa an yi masa magudin zabe a zaben shekarar 2019
  • Godswill Akpabio ya bayyana cewa an yi masa magudin zaben ne domin hana shi yin nasarar lashe kujerar sanata
  • Sai dai, bayanai sun nuna cewa babu kamshin gaskiya a cikin ikirarin da shugaban majalisar dattawan ya yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya sake jaddada cewa shi ne wanda aka zalunta, ba wanda ya ci gajiyar magudi ba a zaben 2019.

Sai dai, shaidun kotu da rahotannin manema labarai sun nuna akasin hakan.

Akpabio ya ce an masa magudin zabe a 2019
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Sai dai rahotannin jaridar Premium Times sun bayyana yadda Farfesa Peter Ogban, malamin jami’a wanda ya kasance jami’in tattara sakamakon zabe a mazabar, ya yi magudi domin amfanin Akpabio.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin, Sanata Akpabio yana takarar neman wa’adi na biyu karkashin jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Majalisa ta yi karin haske kan bukatar dawo da zaben 2027 zuwa 2026

Kotu ta hukunta Farfesa kan magudin zabe

A watan Maris 2021, babbar kotun jiha da ke Ikot Ekpene, Akwa Ibom, ta same shi da laifin canza sakamakon zabe da kuma wallafa sakamakon karya a kananan hukumomin Oruk Anam da Etim Ekpo.

Kotun ta yanke masa hukuncin shekaru uku a gidan yari.

Bayan hukuncin, Akpabio ya nesanta kansa da Farfesa Ogban, yana cewa hukuncin da aka yanke masa ya tabbatar da cewa shi (Akpabio) ba ya da hannu cikin magudin.

Akpabio ya kuma zargi tsohon kwamishinan zabe na INEC a jihar Akwa Ibom, Mike Igini, da hada baki da wasu domin hanashi nasara a zaben.

Akpabio ya juya maganarsa

Sai dai kusan shekaru hudu bayan haka, Akpabio ya juya maganarsa, inda ya ce yanzu Farfesa Ogban ba mai laifi ba ne, sai dai wanda aka zalunta.

Jaridar The Punch ta ce a yayin zaman majalisar dattawa na ranar Alhamis, 16 ga watan Oktoban 2025, Akpabio ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Amupitan: Sabon shugaban INEC ya fadi shirinsa kan sahihin zabe a gaban majalisa

"An yi min magudi a zaben 2019. An gurfanar da wanda bai kamata ba. Idan mutumin yana kokarin taimaka min, me ya sa za su kona kuri’ata a yankina? Me ya sa ba a bayyana ni a matsayin wanda ya yi nasara ba?”

Menene abin da ya faru kan magudin zaben?

Sai dai a zaman kotu, Farfesa Ogban ya amince cewa ya canza sakamakon zaben domin bai wa APC karin kuri’u da ragewa PDP a Oruk Anam.

An zargi Akpabio da kantamo karya
Godswill Akpabio a zauren majalisa Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Lokacin da lauyan gwamnati yake masa tambayoyi, Ogban ya yarda cewa sakamakon da ya rubuta bai fito daga wajen tattara kuri’u na gaskiya ba, sai dai ya ce an karanta masa ne daga bakin jami’an tattara sakamakon kananan hukumomin.

Sai dai, shaidu biyu daga INEC, wato John Enoidem da Itemobong Ekaidem, dukkan su malaman jami’a, sun karyata hakan, suna cewa ba sakamakon da suka gabatar masa ba ne ya rubuta.

A ranar 30 ga Afrilu, kotun daukaka kara da ke Calabar ta yi kashedi ga Farfesan, tana cewa ba hujja ba ce cewa an karanta masa kuri’un magudi.

Duk da cewa an yanke masa hukuncin shekaru uku, Farfesan ya ci gaba da yawonsa bayan da ya roki afuwa a gaban kotu, yana mai cewa ya koyi darasi.

Kara karanta wannan

Surukar Akpabio ta ballo ruwa, ta jingina Shugaban Majalisa da kashe jama'a a Akwa Ibom

An yi zargi kan Akpabio

A wani labarin kuma, kun ji cewa kanwar matar shugaban majalisar dattawa ta yi zarge-zarge kan mijin yayarta.

Ta yi zargin cewa Godswill Akpabio yana da hannu kan kisan wasu bayin Allah lokacin da yake gwamna.

​Hakazalika ta bayyana cewa baya ga kashe mutane yana Gwamna, Akpabio ya na da masaniya a kisan wadansu bayin Allah bayan ya shiga majalisa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng