Kebbi: An Ji Gaskiyar Zance kan batun Jawo Sojojin Haya don Yaki da 'Yan Bindiga

Kebbi: An Ji Gaskiyar Zance kan batun Jawo Sojojin Haya don Yaki da 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin jihar Kebbi ta yi magana kan rahotannin da ke cewa ta dauko hayar sojoji daga kasashen waje don yaki da 'yan bindiga
  • Ta bayyana cewa ko kadan ba ta kulla wata yarjejeniya da kamfanonin kasashen waje ba don yaki da 'yan bindiga
  • Hakazalika, ta nuna cewa za ta ci gaba da bakin kokarinta wajen tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al'umma

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta yi martani kan rahotannin da ke cewa ta dauko hayar sojoji daga kasashen waje don yaki da 'yan bindiga.

Gwamnatin Kebbi ta karyata rahotannin masu cewa ta ɗauko hayar mayakan kasashen waje don yaki da ‘yan bindiga da sauran miyagun laifuffuka a jihar.

Gwamnatin Kebbi ta musanta dauko hayar sojojin kasashen waje
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris. Hoto: @NasirIdrisKIG
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Ahmed Idris, ya fitar a ranar Juma’a, 17 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamna Bago ya samo hanyar magance 'yan ta'adda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me gwamnati ta ce kan dauko hayar sojoji?

Ya bayyana labarin a matsayin karya, yaudara da rashin makama, inda ya roki jama’a da su yi watsi da shi baki ɗaya.

Wannan musantawar ta zo ne bayan wani rahoto da ke cewa gwamnatin jihar ta yi hadin gwiwa da kamfanin tsaro na kasar China mai suna G-Safety domin taimaka mata wajen yakar ‘yan bindiga da masu aikata laifuffuka.

Sai dai, a cewar Ahmed Idris, gwamnatin Gwamna Nasir Idris ba ta taɓa sanya hannu kan wata yarjejeniya ko kwangila da wani kamfanin tsaro na kasashen waje ba.

“Hankalin gwamnatin jihar Kebbi ya kai kan wani rahoton da ke yawo a kafafen yada labarai cewa ta ɗauki hayar wani kamfanin tsaro na kasar China, G-Safety, domin yaki da ‘yan bindiga da sauran laifuffuka."
“Gwamnati na son ta bayyana a fili cewa babu irin wannan yarjejeniya ko kwangila da aka kulla da wani kamfanin tsaro na kasashen waje.”

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun lallaba cikin masallaci ana sallar asuba, sun sace mutane

- Ahmed Idris

Gwamnatin Kebbi na kokarin samar da tsaro

Ahmed Idris ya tabbatar da cewa Gwamna Nasir Idris yana ci gaba da inganta haɗin kai da hukumomin tsaron cikin gida domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duk fadin jihar.

Gwamnatin Kebbi ta yi bayani kan dauko hayar sojojin haya
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, yana addu'a. Hoto: Nasir Idris Kauran Gandu
Source: Facebook

Ya kara da cewa tsaro na daga cikin manyan abubuwan da gwamnati ke bai wa muhimmanci, inda ake ɗaukar matakai daban-daban don tallafawa aikin sojoji da kuma shirye-shiryen al’umma na dawo da zaman lafiya a yankunan da rikice-rikice suka shafa.

Haka kuma, ya shawarci ‘yan jarida da kafafen watsa labarai da su tabbatar da sahihancin bayanai daga hukumomin gwamnati kafin wallafa su, domin guje wa yada bayanan karya da ka iya rikita jama’a.

“Manufarmu ita ce tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, ba maida hankali kan labaran da ba su da tushe ko kuma maso kawo ruɗani a tsakanin jama’a ba."

- Ahmed Idris

Gwamnatin Kebbi ta musanta kai harin 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kebbi ta jawo kamfanin kasar China domin taya ta yaki da Lakurawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta musanta rahotannin da ke cewa 'yan bindiga sun kai wani kazamin hari.

Ta bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya kan harin da ake cewa 'yan bindigan sun kai a kauyen Makuku.

Gwamnatin ta bayyana cewa lamarin ya auku ne a wani kauye da ke jihar Neja mai makwabtaka da ita.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng