Diri: Jam'iyyar APC Ta Fara Zawarcin Gwamnan da Ya Fice daga PDP, Ta Bayyana Dalili
- Tsohon dan majalisa Sunny-Goli ya bayyana cewa APC na fatan Gwamna Douye Diri zai koma cikinta bayan barin PDP
- Sunny-Goli ya ce ya kada kuri’a ga Diri duk da kasancewarsa dan APC saboda ya na da nagarta, kuma ya kawo ci gaba
- A ranar Laraba ne dai Gwamna Diri ya fice daga PDP amma bai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai shiga ba tukuna
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon dan majalisar wakilai kuma jigo a jam’iyyar APC a Bayelsa, Hon. Israel Sunny-Goli, ya yi magana kan sauya shekar Gwamna Douye Diri.
Hon. Israel Sunny-Goli ya bayyana cewa akwai yiwuwar Gwamna Douye Diri ya koma jam’iyyar su ta APC nan ba da jimawa ba.

Source: Twitter
APC na maraba da Gwamna Diri
Tsohon dan majalisar ya bayyana haka ne yayin hira da Channels TV a shirin 'Siyasa a Yau' a ranar Alhamis, bayan Diri ya sanar da ficewarsa daga PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan siyasar ya ce matakin da Gwamna Diri ya dauka ya nuna cewa ya shirya fara bin sabuwar hanyar siyasa da za ta dace da ci gaban al'ummarsa.
Ya kara da cewa dukkan shugabannin APC a jihar Bayelsa suna maraba da yiwuwar zuwansa, ganin irin salon shugabancinsa da ya dace da tsarin jam’iyyar.
‘Muna addu'ar Diri ya koma APC’
Sunny-Goli ya bayyana cewa shi da sauran shugabannin jam’iyyar APC a Bayelsa suna kan rokon Ubangiji ya sa Gwamna Diri ya shiga jam’iyyarsu.
A cewarsa, Diri gwamna ne mai hangen nesa, gaskiya da kishin kasa, kuma ayyukan ci gaba da yake gudanarwa sun tabbatar da hakan.
“Mun ga ayyukan da yake yi a jihar, kuma muna ganin shi ne gwamna mafi nasara da jihar ta taba samu, shi ya sa muke so ya shigo cikinmu.”
- Hon. Israel Sunny-Goli.
Ya kuma ce tarihi zai yi wa Diri adalci bayan kammala mulkinsa, domin zai bambanta da wadanda suka gabace shi wajen aiwatar da ayyuka.
Sunny-Goli ya zabi Diri a zaben 2023
Tsohon dan majalisar ya ce duk da kasancewarsa dan jam’iyyar APC, ya kada kuri’a ga Gwamna Diri a zaben gwamna na baya.
Da yake kare matakinsa, Sunny-Goli ya gwamnan ya nuna gaskiya da kwarewa a tafiyar da mulki, kuma shi ba ya yin adawar da ta wuce gona da iri.
Ya kuma yi watsi da jita-jitar cewa Diri zai koma jam’iyyar LP ko ADC ta 'yan hadaka, yana mai cewa jam’iyyun ba su da karfi da tsari irin na APC.

Source: Facebook
Gwamna Diri ya fice daga PDP
Tun da fari, mun ruwaito cewa a ranar Laraba, Gwamna Douye Diri ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP a dakin taron majalisar zartarwa ta jihar Bayelsa.
Gwamna Douye Diri ya ce ya yanke wannan shawara ta barin PDP ne bayan dogon nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki a jihar.
Sai dai ko a lokacin, bai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai shiga ba, amma magoya bayansa na ganin cewa zai koma APC nan ba da jimawa ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

