Gwamnatin Tinubu Ta Jero Abubuwan da Suka Jawo Karyewar Farashin Abinci Warwas

Gwamnatin Tinubu Ta Jero Abubuwan da Suka Jawo Karyewar Farashin Abinci Warwas

  • Gwamnatin tarayya ta ce karin samar da amfanin gona da fitar da kayan da da 'yan kasuwa suka boye ya haifar da saukar farashi
  • Ministan noma, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ya ce shirin gwamnatin shugaba BolaTinubu ya fara haifar da sakamako a fannin noma
  • Ya ce gwamnati Najeriya ta samar da tallafi da kayan noma don rage farashin kayan abinci da tabbatar da wadatarsa ga ’yan kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.


FCT, Abuja Abuja – Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa daya daga cikin dalilin da ya sa farashin kayan abinci ke sauka a kasuwanni shi ne yawaitar amfanin gona.

Karamin ministan noma, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana haka a lokacin taron manema labarai na bikin Ranar Abinci ta Duniya ta 2025 a Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kebbi ta jawo kamfanin kasar China domin taya ta yaki da Lakurawa

Wasu kayan abinci a kasuwa
Buhunan kayan abici a wata kasuwa. Hoto: Garba Muhammad
Source: Facebook

Leadership ta rahoto ya ce sakamakon sauye-sauyen da ake yi a fannin noma da tsayayyen tsarin gwamnati ya fara bayyana, inda manoma ke samun karin amfanin gona a wannan shekarar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati: "An samu karin amfanin gona"

Abdullahi ya bayyana cewa binciken aikin gona na lokacin damina na 2025 da cibiyar NAERLS ta gudanar ya nuna karin amfani kamar shinkafa, masara, rogo, dawa, gero, doya da wake.

Business Day ta wallafa cewa ya ce hakan ya biyo bayan kokarin gwamnati da shirin tallafa wa manoma a karkashin shirin Renewed Hope na shugaban kasa.

Ministan ya kara da cewa gwamnati na amfani da hanyoyi da dama don tabbatar da wadatar abinci a farashi mai sauki, ta hanyar tallafin taki, bashi mai sauki da amfani da injinan noma.

Dalilin saukar farashin abinci warwas

Abdullahi ya ce an fara samun saukin farashin abinci ne daga tsoron da ’yan kasuwa suka ji bayan gwamnati ta sanar da shirin shigo da dan kadan daga kasashen waje domin cike gibi.

Ya ce hakan ya sanya ’yan kasuwa suka fitar da kayan da suka boye, wanda ya kara yawan kayan abinci a kasuwa, ya rage karancin da ke haifar da tsadar kayayyaki.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Bello Turji na shirin kai sababbin hare hare a wasu garuruwan Sokoto

Karamin ministan noman Najeriya
Karamin ministan noma, Aliyu Sabi Abdullahi. Hoto: @sabialiyu
Source: UGC

Duk da haka, ya bayyana cewa shigo da abinci bai yi tasiri sosai ba kamar yawaitar amfanin gona a cikin gida da ya wadatarsa a kasuwa.

Ministan ya ce yawan amfanin gona, fitar da kayan da aka boye, da damina mai kyau da aka samu ne suka jawo saukin farashin abinci a kasuwanni.

Saukar farashi: Minista ya ce jihohi na taka rawa

Ministan ya ce gwamnatocin jihohi suna taka muhimmiyar rawa wajen kafa wuraren ajiye abinci domin daidaita farashin kaya idan ya tashi.

Ya kawo misali da jihohin Kaduna, Kano, Jigawa da Neja wadanda suka kafa wajen ajiya domin tallafawa jama’a a lokacin tashin farashin kayan abinci.

Sabi ya kara da cewa domin rage asarar manoma sakamakon saukar farashi, gwamnati na ba su kayan aikin noma kyauta ta hannun kungiyoyin manoma da matasa.

Makiyaya sun hana noma a Darazo

A wani rahoton, kun ji cewa wani rikicin manoma da makiyaya ya jawo hana mutane zuwa gona a karamar hukumar Darazo, Bauchi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a sabon harin da suka kai garuruwan Filato

Rahotanni sun nuna cewa an fara rikicin ne bayan gwamnatin jihar Bauchi ta ware wasu filaye domin yin noma.

Manoma a karamar hukumar sun yi kira ga gwamna Bala Muhammad da ya dauki matakin da ya dace domin magance matsalar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng