Sarki Sanusi II Ya Dura China, Ya Gana da Kamfanoni domin Kawo Cigaba Kano

Sarki Sanusi II Ya Dura China, Ya Gana da Kamfanoni domin Kawo Cigaba Kano

  • Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya ziyarci kasar China domin jawo masu zuba jari a bangaren makamashi da tsaro a jihar Kano
  • An karɓe shi cikin girmamawa a kamfanonin POWERCHINA Huadong da kuma Dahua Technology da ke birnin Shanghai
  • Ziyarar ta zo ne bayan irinta da Sarki Sanusi II ya yi a Amurka da Tunisiya domin cigaban Kano da Najeriya baki ɗaya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.


China – Khalifa Muhammadu Sanusi II ya kai ziyarar aiki a kasar China domin ci gaba da kira ga masu zuba jari a bangaren makamashi da tsaro.

Sarkin ya samu tarba mai girma daga manyan kamfanonin kasar, ciki har da HEDC da Dahua Technology, kamfani mai kwarewa a fannin fasahar tsaro.

Sarki Sanusi II da wasu 'yan China
Sarki Muhammadu Sanusi II bayan ganawa da wasu 'yan China. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan abubuwan da 'yan China suka tattauna da Sanusi II ne a wani sako da masarautar Kano ta wallafa a X.

Ziyarar ta kasance wani bangare na kokarinsa na ganin an kara habaka tattalin arziki da ci gaban masana’antu a Kano da ma Najeriya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a sabon harin da suka kai garuruwan Filato

Muhammadu Sanusi II ya je taro China

A ranar 15, Oktoba, 2025, Sarkin Kano ya halarci taron WFEO a birnin Shanghai, inda shugaban kungiyar, Mustapha Shehu, wanda shi ma dan asalin Kano ne, ya jagoranci zaman.

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasar China da wasu fitattun shugabanni daga kasashe daban-daban.

A wajen taron, Sarkin Kano ya bayyana muhimmancin hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya domin habaka ci gaban fasaha da makamashi, musamman a nahiyar Afrika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadin gwiwa da manyan kamfanonin China

A yayin ziyararsa, Khalifa Sanusi II ya gana da shugabannin kamfanin Dahua Technology, inda aka tattauna kan dabarun tsaro da hanyoyin da za su inganta tsaron Kano.

Kamfanin na daya daga cikin manyan cibiyoyin samar da kayan fasahar tsaro a duniya, wanda ke kwarewa da amfani da na’urorin zamani wajen gano laifuffuka da kare jama’a.

Sanusi II tare da wasu 'yan China
Sarki Sanusi II yana magana da jami'an kamfanonin China. Hoto: Sanusi II Dynasty
Source: Facebook

Masarautar ta bayyana cewa tattaunawar da aka yi za ta kawo sakamako mai kyau, musamman wajen yaki da miyagun laifuffuka da samar da tsaro ga jama’ar Kano.

Kara karanta wannan

'Abba na aiki,' Manyan abubuwan alheri 4 da suka samu jihar Kano a shekarar 2025

Cigaban makamashi da albishir ga Kano

A cewar Sarkin Noman Sarkin Kano, Malam Ahmad Husain, ziyarar ta kunshi tattaunawa kan inganta wutar lantarki a jihar Kano.

Ya ce kamfanonin China sun nuna shirin hadin kai da gwamnatin Kano domin samar da sababbin tsare-tsare da za su bunkasa samar da makamashi.

Husain ya kara da cewa mutanen Kano za su amfana matuka da wannan ziyarar, kasancewar tana da jagorori masu hangen nesa kamar Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarki Sanusi II.

Sarki Sanusi II ya yaba wa Bola Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Muhammadu Sanusi II ya jinjinawa shugaba Bola Tinubu kan cire tallafin mai.

Sarkin ya bayyana cewa matakin da shugaban kasar ya dauka ya taimaka wajen daidaita tattalin arzikin Najeriya.

Sanusi II ya ce a yanzu haka Najeriya ta haura tudun mun tsira kan matsalolin tattalin arziki, domin a cewarsa, za a fara ganin cigaba saboda matakan Tinubu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng