Daya daga cikin Manyan Yan Kasuwa da Suka Horas da Abdussamad BUA Ya Rasu

Daya daga cikin Manyan Yan Kasuwa da Suka Horas da Abdussamad BUA Ya Rasu

  • An shiga jimami bayan sanar da rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma mai kera kayayyaki bayan fama da jinya mai tsawo
  • Marigayin Alhaji Ali Oladeinde Akinyele shi ne ya kafa kamfanonin AkinOcean Nigeria da Allison Foam a Najeriya
  • Marigayin da ya fito daga gidan sarauta a Isale Eko, ya fara aikinsa a matsayin mai zane na injiniyanci kafin ya zama babban ɗan kasuwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lagos - An sanar da rasuwar fitaccen dan Kasuwa a Najeriya, Alhaji Ali Oladeinde Akinyele bayan ya sha fama da doguwar jinya.

Fitaccen ɗan kasuwar kuma wanda ya kafa manyan kamfanoni AkinOcean Nigeria da Allison Foam ya rasu ranar Laraba 15 ga watan Oktobar 2025.

Babban dan kasuwa ya rasu a Najeriya
Fitaccen dan kasuwa, Alhaji Ali Akinyele da Abdulsamad Rabiu. Hoto: Yushau Shuaib, BUA Group.
Source: Facebook

Takaitaccen tarihin marigayi Alhaji Ali Akinyele

Rahoton The Nation ya ce an haifi marigayin a ranar 18 ga Afrilu, 1947, a cikin gidan sarauta na Agata Shokun Onilegbale da ke Isale Eko, jihar Lagos.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a sabon harin da suka kai garuruwan Filato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya fara aikinsa a matsayin mai zane kafin shiga harkar kasuwanci inda ya fara aiki a kamfanin Isiaka Rabiu and Sons da ke Kano.

Ya yi aiki a matsayin mai ba da horaswa karkashin jagorancin attajiri Alhaji Isiaka Rabiu.

Yadda marigayin ya horas da Abdulsamad BUA

A lokacin, Akinyele ya horar da matasa da dama a fannin kasuwanci, ciki har da wadanda suka zama manyan ‘yan kasuwa kamar shugaban BUA Group, Abdulsamad Rabiu.

Daga baya kuma ya kafa nasa kamfanonin masu inganci a Najeriya domin bunkasa tattalin arziki da kuma ba matasa aiki, ya bada gudunmawa wurin tabbatar da cewa matasa da dama sun dogara da kansu.

Marigayin ya kasance Musulmi mai rike addini da kuma mai kyautatawa al'umma wanda ya yi suna wajen taimakon al’umma da tallafawa ci gaban ɗan adam.

Ya taimaka wa kananan ‘yan kasuwa da dama su bunƙasa, tare da bayar da gudunmawa ga kungiyoyin addini da na jin ƙai a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan

Duniya labari: Babban malamin addini ya riga mu gidan gaskiya

An yi rashin babban dan kasuwa a Najeriya
Taswirar jihar Lagos da ke Kudu maso Yamma. Hoto: Legit.
Source: Original

Yaushe za a yi jana'izar marigayin?

Alhaji Akinyele ya bar matar sa, ‘ya’ya da jikoki, waɗanda za su ci gaba da kula da kyakkyawan ayyukan da ya yi da kuma gudunmawa da ya bayar kacin da yake raye.

Rahotannin sun tabbatar da cewa za a gudanar da sallar jana’izar marigayin a babban Masallacin Juma'a da ke sakatariyar Alausa, cewar Daily Trust.

Sannan majiyoyi sun ce za a birne gawar marigayin a makabartar Abari da ke jihar Lagos jim kadan bayan idar da sallar jana'izarsa a masallaci.

'Dan kasuwa, Dantata ya rasu a Dubai

Mun ba ku labarin cewa babban ɗan kasuwar Kano, Alhaji Aminu Ɗantata, ya rasu a daren ranar Juma'a, 27 ga Yuni, 2025, yana da shekaru 94 a duniya.

An tabbatar da cewa Ɗantata ya rasu ne a Abu Dhabi, babban birnin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, daga bakin makusantansa, Sanusi Dantata.

Wani tsohon mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Malam Bashir Ahmad, ya ce Kano da Najeriya sun yi babban rashin dattijo.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.